Labarai

Ƴan sanda sun saki miji, sunyi cafke wanda ake zargi da kashe matar aure a borno

Rundunar ƴansanda a jihar Borno, a jiya Talata ta ce ta saki mijin matar da aka kashe a gidan aurenta da ke Maiduguri bayan ta kama babban wanda ake zargi.

Rundunar ƴansandan ta ce an sako mijin marigayiyar, mai suna Adamu Ibrahim da abokinsa, Bukar Wadiya da aka tsare su bayan sun kai rahoton afkuwar kisan ga ƴansanda.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito,Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta ASP Sani Kamilu.

Ƴan sanda sun saki miji, sunyi cafke wanda ake zargi da kashe matar aure a Borno
Ƴan sanda sun saki miji, sunyi cafke wanda ake zargi da kashe matar aure a borno

Ya ce an bi sawun babban wanda ake zargin, Abacha Bukar tare da kama shi da laifin kisan matar mai suna Fatima Alhaji-Bukar mai shekaru 24 a ranar 18 ga watan Oktoba.

Kamilu ya ce ƴansanda sun kama wanda ake zargin ne bayan da suka bibiyi wayar marigayiyar da ya sace.

Ya ce an kuma kama wasu mutane biyar da ake zargi da karbar sauran kayayyakin da aka sace a yayin kisan da kuma hada kai wajen aikata laifi.

A cewarsa, sauran wadanda ake zargin sun hada da Ibrahim Mustapha, Usman Yusuf, Muhammed Yunus, Nuhu Mohammed da Ismaila Mohammed Barka duk a yankin Gwange na Maiduguri.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button