Kannywood

Zargin shan jini yadda ta kaya tsakani kamaye da wani yaro da yayi masa ƙazafi

Wannan al’amarin na zargin wasu mutane suna jan jini inda yayi ƙamari a arewacin najeriya shine majiyarmu ta samu wani labari daga shafin dan jarida Nasiru Salisu zango inda ya wallafa al’amarin da ya shafin babban marubucin nan kuma jarumi kamaye ga yadda ta kaya.

Wannan iya shegen da ake na cin zarafin Mata bisa zargin suna Shan jini ya dade a kasar nan domin a shekaru 20 da suka gabata, Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan gurasa da aka fi sani da kamaye yaje gun Abokin sa (Usaini Sule Koki) yana zuwa sai ya taba Kan wani Yaro yace”Jeka Kayi min Sallama da Malam Usaini”Ai kawai sai yaron ya kwalla Kuka wai an sace masa Linsayayninsa nan take aka cika za’a kashe kamaye Allah ya taiamaka aka samu masu hankali aka shiga makaranta mutane kuma na cigaba da taruwa a waje sun tanadi fetur da taya suna jira a fito dashi su babbake shi.

Ana haka sai babar yaron tazo tana ta tumami tana Kuka har da tayar da iskokai, anan ne wani ya gane kamaye yace wannan fa marubucin litattafan nan ne Dan’azumi Baba Chediyar’yan gurasa,nasan shi,Ai kuwa sai wani yace ai zaka iya sanin mutun yau washe gari kuma ya sauya. Da yake makaranta ce a gun sai shugaban makarantar yace a dakata ya kalli kamaye yace gaskiya, Malam Ba domin mun ganka da shiga ta kamala ta Hausawa ba, da ba haka ba, amma ta yaya kayi wannan abu? Kamaye yace
“Wallahi babu abin da nayi masa “ Duk wannan Abu fa babu Wanda yayi tunanin a Kira Usaini Sule koki a tambaye shi,kuma babu Wanda yayi tunanin a tube wandan yaron a gani. Kowa kawai ya yadda da abin da Dan kankanin yaro ya fada, so yake kawai a hallaka mutum babu hakki .Zargin shan jini yadda ta kaya tsakani kamaye da wani yaro da yayi masa ƙazafi

To ana cikin haka ne sai Kakan yaron yazo, yana zuwa aka bude masa ya shiga, ya kalli Kamaye yace Malam me ya faru,sai ya gaya masa abin da ya faru, nan take sai yace “ to shin ma an bude wandon yaron an gani “ Nan da nan kuma sai Kowa ya fara zare Ido ,Dattijo ya cire wandon yaro sai gashi komai yana nan a mazaunin sa intact.

Nan dai Kowa jikin sa yayi sanyi,amma duk da Haka sai da wani yace Ai wai Kamayen yaga wuya ne ya dawowa da yaron kayan sa.

Ko a jiya mun yi hira da Kamaye ya sake nanata min wannan labarin.
Wannan fa yana nuna cewar Kai da kake dagewa cewar Mata suna Shan jini a kaddamar musu wata ran Kai Ma idan Kayi fitar kafa kaje unguwar da ba’a san kaba, za’a iya cewar kasha jini, Koma watakila gyatumar ka tayi batan Kai a wata unguwar idan ta tambayi hanya ace jini zata sha.
Dan Allah Mu kiyaye, Allah ya raba mu da duhun jahilci.

Ga firar da ankayi da kamaye nan.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button