Zaluncin rusa zaben Abba Gida-gida ya sanya ni tunanin barin Nijeriya – Ali Jita


Bayan yanke hukunci sakamakon zaɓen gwamnan Kano Engr Abba Yusuf inda kotu ta anya Dr. Nasiru yusuf gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben jihar kano da ratar kuri’a dubu talatin da shidda bayan kotun ta cire kuri’un abba kabir Yusuf dubu dari da sittin da biyar da yan canji akan cewa haramtattun kuri’u ne.
Jarumai da mawaka, furodusa da daraktas a masana’atar kannywood masu ra’ayin NNPP sunyi tsokaci sosai akan irin wannan hukunci da ankayi musu marar daɗi.


A yau jaridar Dclhausa kamar yadda sunka saba suna gayyato bakinsu a cikin wannan zare domin tattaunawa da su akan jin ta bakinsu a wannan sati fitaccen mawakin ne Ali Isah wanda ankafi sani da ali jita shine bakon shirin yadda ya bayyana ra’ayinsa akan hukuncin kotu.
” A gaskiya ni tun farko da ankayi wannan hukunci cewa nayi na hakura da Najeriya tattara inawa inawa da zai yuyi in bar kasar duk wani buri “hope” da talaka yake da shi an ruguza shi , kana ji malamai na cewa idan an shiga wani bala’i ko uquba suce a koma ga Allah.
Tayaya zamu koma ga Allah mu zabi mutanen kirki taya za’a yi talaka tun shekarar 2019 da gwamnati batayi musu ba, su zabi wandanda suke gani mutanen kirki wadanda zasu zo su gyara mana, farkon wa’azin malamai cewa suke ku zabi mutanen kirki in kuna so kasa ta gyaru .
Ba’a bayarda anka kwace, mutane talakawa su kayi hakuri sukayi azumin shekara hudu 4 , ta dawo kwan su da kwar-kwatasu sunka dawo suka son su canza Wannan gwamtani da suke gani ta zalunce su ko tana zaluntar su, amma har yanzu mutanen nan suka ƙi hakura suka zo suka kwace mulkin nan.
To ya kake tunanin mutane zasuyi , siyasa mun shigeta ba dan mu ba, inaso kayiwa mawaka musamman irinsu rarara kaji, shin dan ma miye suke siyasar .
Shin sun shiga siyasa ne domin mutane ko domin kansu.
Ali jita ya kara da cewa ina tabbata maka ko gobe za’a sake zaɓe abba gida gida ne zai ci zaɓe zan iya gitta rayuwata kamar yadda hajiya najaatu ta fada , tun kafin ayi zaben sunce in kuri’a daya tak ta ishe su, daman ba cin zaben ne a gabansu ba sun yi shiri tayaya zasuyi rikici tun wurin zaben a tashi zaben in wannan bai yiyu ba, taya zasu hana a kirga, in wannan bai yiyu ba ina gaya suna da shiri “plan” A har zuwa D. -inji mawaki Ali jita.
Ga bidiyon nan domin ku saurara.