Yanzu- Yanzu: Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu
Innalillahi wainnailaihim rajiun a yanzu nan majiyarmu ta samu mummunan labari marar dadi wanda shafin Abubakar Abdullahi Giro argungu sunka wallafa rasuwar babban malamin nan Sheikh Abubakar Giro Argungu.
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN!
Allah Yayiwa Sheikh Giro Argungu Rasuwa, Bayan Jinya Da Ya Samu A Daren Jiya, Bayan Kammala Tafsir Magriba Zuwa Ishaa, Allah Yayi Maka Gafara Sheikh Amin..
Wednesday!
6th September, 2023.”
Za’a gabatar da sallar janazan da misalin karfe biyu na rana (2:00pm). A masallacin Idin Sarki dake garin Argungu a jahar kebbi, Naijeriya.
Muna addu’ar Allah ya jikanshi ya gafarta mashi ya sanya Aljannah ta zamo makoma a gareshi. Mu kuma ya kyautata ta mu idan ajalin mu yazo
إن لله ما أخذ وله ما أعطى وكل شيء عنده بأجل مسمى