google-site-verification=WmtThtgKMuimwQoXo8Cd4z9ZhII1jY-1XVfjGSvL5r8
Labarai

Yan bindiga sun kashe mutun hu’du mun Kuma sace mutun talatin a jihar sokoto

Hukumomin ‘yan sanda a jihar Sokoto sun tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Giyawa da ke karamar hukumar Goronyo da ke gabascin jihar sokoto inda sun ka tafi da mutane talatin ko sama da hakan da kuma kashe mutum hudu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, mataimakin Sufeto Ahmed Rufa’i, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa maharan sun yi awon gaba da mutane goma sha takwas da farko wadanda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da dabbobi.

Sai dai ya ce bakwai daga cikin wadanda aka sacen sun tsere sun koma yankinsu inda mazauna yankin da dama suka gudu domin tsira.

Ko da yake wasu majiyoyi daga al’ummar da abin ya shafa sun yi ikirarin cewa an yi garkuwa da mutane sama da 30, ‘yan sandan sun ci gaba da cewa mutum goma sha daya ne kawai ke tare da maharan.

Hukumar tsaron ta ce jami’ansu na nan suna bin maharan kuma suna kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a cikin al’umma da kewaye.

Dan majalisa mai wakilta Gada da Goronyo Cmrd Bashir Gorau ya ya jajantawa al’ummarsa da alhijin abunda ya faru inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Yan bindiga sun kashe mutun hu’du mun Kuma sace mutun talatin a jihar sokoto
Honourable Cmrd Bashir Gorau

Nayi matukar bakin ciki da jin labarin abubuwan da suka faru daren jiya cikin al’ummarmu na hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Goronyo, wanda ya yi sanadin hasarar rayukka biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane fiye da 30.

A wannan lokaci na bakin ciki, addu’o’inmu da tunaninmu na tare da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu. Muna addu’ar Allah SWA Ya jikan wadanda suka rasu Ya kuma baiwa iyalansu haƙuri da kuzari a wannan mawuyacin lokaci.

A matsayina na wakilin ku, ina so in tabbatar muku da cewa zamu cigaba sosai wajen tabbatar da tsaron rayukka da dukiyoyin ku. Zan yi duk abunda ke yiyuwa ba tare da gajiya ba, Haka Kuma zamu cigaba da hada Kai da hukumomin da abin ya shafa, don magance wannan matsalar tsaro.

Mu tashi tsaye mu goyi bayan juna a wannan mawuyacin lokaci. Tare, za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen tsaron domin amintarda al’ummomin mu.

Allah SWT Ya tsare mu baki daya, Ya bamu ikon jure wadannan wahalhalu. Amin”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button