#Wuff: Shin ko kun san cewa wannan zankaɗeɗiyar budurwa ba auren jari tayi ba
Duba da irin yadda tsada rayuwa ta ke a Nijeriya da kuma yadda abubuwa suke ta tashi sosai amma abun a yaba sai gashi sadakin wannan kyakkyawar budurwa tayi arha, ko wadanda basu kaita kyau ba madaidaita ana yanke sadakinsu #100,000 amma ita abun Masha Allah abin ayi koyi.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga wani shafin mai suna wakiliya ta ruwaito mahaifiyar yarinyar ta fadi cewa ba auren jari sunka ba ga yadda rahoton ya fito.
Mahaifiyar wata amarya ta fito ta yi bayani bayan an fara yaɗa hoton ta a kafafen sadarwa ana cewa auren Naira ta yi,
Wakiliya ta ruwaito, Hajiya Mairo mahaifiyar Rukayya Sadauki wacce ta amarce da angonta Umar a makon da ya gabata a wani kayataccen biki ta ce.
” Alhamdulillah, yara na sun samu tarbiyya “are well trained”, masu sharri ya kare a kanku!
You will be surprised to know that (za kuyi mamaki idan na faɗa maku) sadakinta is 58k (dubu 58 ne) ango da kansa ya ƙara zuwa 100k! (Dubu ɗari).
Allah ya ba ku zama lafiya. Ya yi maku albarka amin.
Masu cewa muna sa dogon buri akan yaranmu kun ji kunya kuma In Shaa Allah kuna kan ji! Munafurci dodo!” Injii Hajiya Mairo.
Dalilin fadin mahaiyar irin yadda al’umma a kafar sada zumunta ke nuna cewa ka nemi kuɗi domin kuwa komai tsufanka zaka auri zankaɗeɗiyar budurwa son kowa ƙin wanda ya rasa.