“Wallahi Tallahi” Gawuna bazai yi mulkin Kano ba – Cewar sunusi oscar


A yau ne kotun sauraren karar ta bayyana nasiru yusuf gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben jihar kano.
Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.


Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir, bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 18 ga watan Maris na 2023.
Kotun ta bayyana wannan hukunci ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro.
Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugabar kotun mai alƙalai guda uku.
Shine mai baiwa Gwamna Shawara ta musamman a bangaren kannywood Sunusi oscar ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta yake cewa
” Wallahi tallahi Gawuna bazai mulkin Kano ba.
Inaso mai girma gwamna ya bani dama”
A kasan rubutu ya sake wallafa cewa.
“Na rantse da wanda ya busan numfashi GAWUNA bazai mulki KANO BA, Inada Hujjojina.”
Mutane sunyiwa mai baiwa Gwamna Shawara ta musamman a bangaren kannywood kamar haka.
@Hassan Yusuf gama yana cewa :
To nikam ranka ya dade me ka taka ne haka
@aljaninahfy yana cewa : Maganar banxa ce wai ace gawuna ne yaci mulkin kano.
@official_ibraheem_fafa yana cewa :
Oscar abi komai a hankali Allah shine mafi karfi a kan kowa.
@imamu galazy cewa yake : Allah shi kadae yasan gaibu. Kar duniya tasa mu rasa imaninmu, shi mulki ai na Allah ne kawae muyi addu’ar alkhairi.
@ba_suna_1 yana cewa : Duk Nigeria Ba Wanda Yakai Ganduje Makirci Da Manafirci Kuma Allah Ya Isa.