AddiniLabarai

“Wallahi billahi” mafi yawan mata masu online Business mazina ta ne – cewar sheikh Abdallah Adam

A wajen majalisi malam abdallah Adam yayi wani nasiha zuwa ga iyaye mata da maza akan su sanya ido akan ya’yansu masu cewa suna online business ku sanya ido sosai domin yanzu sun lalace duba da irin yadda yarinya zata tashi zuwa kaiwa wanda ya saye kaya bata san halinsa ba.

Malamin ya fadi maganar ne a wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta ga abinda malam yake cewa.

“Wallahi, Billahi, Tallahi an ɓata ‘ya’yan mutane anyi zina da su ta wannan hanya da yawan tsiya, wai yarinya tanayin donot ko tanayin chinchin ko tanayin wani fanke ko cake sai ta sanya a WhatsApp dinta ko facebook dinta, sai ta sanya order yan iska ne mafi yawa na rantse da Allah.

Sai ta bada order sai wanda yayi order yace yana otal kaza saboda mala’ika jibrilu ne yayi aike kizo ki kawomin order ta.

Malam ya kara da cewa : Wallahi, Billahi, Tallahi an ɓata ‘ya’yan mutane anyi zina da su ta wannan hanya da yawan tsiya, karka yadda ‘yarka tace maka ae business ta fara karya take yar iska ce.

Matan annabi basuyi sana’a ba, fita suke ko zuwa gida ake a saya to Shikenan sai a zo a saya, iyayenmu sun taso suna sana’a sai su dorawa yaro yaje talla ko kazo gida ka kwankwasa kofa yaro yazo ya sayoma abinda zaka saya, amma yanzu matan yanzu za’a placing order shikenan dan iska order biyu yayi, dan iskan yayi order din kayan yayi order mai kayan.

Kasan wallahi wannan yan duniya dauka suke bamusan me muke yi ba, wannan ba wayo zakayiwa Allah ba duk kokarin da kayi na lalata yar wani ka jira me zai faru da yarka ko babarka, kana sakaren banza baka san me ke faruwa a cikin iyalinka ba.

Malam ya kawo aya Alkur’ani da ke cewa Allah yana cewa : “kuyi korakin kange kawunanku  daga shiga wuta da iyalenka“, duk abinda yarka zatayi ka sanya mata sharadi da ka’ida don kar ace mun hana sana’ar ‘ya’ya mata , a’a suyi Sa’a amma asa dokoki idan kanenta zai kai mata, idan super market ne ya kai mata.

Amma a sa sharudda kada abari ta tafi da kanta, wai wata idan zataje kai placing order sai ta sanya babbar riga munafukar Allah ta’ala sai ta sanya doguwar riga tayi kwalliya ta sanya jan baki a fesa turare sai ta kira mai keke napep dinta, wai yanzu fah yan mata kowa nada mai napep dinta – inji malamin.

Ga bidiyon nan ga mai bukata sai ya saura .Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button