Tsoho da kuɗi yaro : Kyakkyawar Mata Ta Nunawa Duniya Mijinta Dan Dattijo a Bidiyo
Wata matashiya yar Najeriya wacce ta aure wani dattijo ta haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya yayin da ta baje kolin mijinta.
Matashiyar, @asmawu.hamisu, ta kira dattijon da “rayuwata” sannan ta rike hannunsa a kan teburin cin abinci yayin da suke bidiyon a TikTok. Jaridar legit hausa na ruwaito.
Matashiya da dattijon mijinta
Alamu sun nuna mijin yana da sanyin hali yayin da matashiyar take ta matso kyau a gaban kamara. Binciken da aka gudanar a shafinta na TikTok ya nuna tana jin dadin rayuwa tare da murza kudi yadda take so.
A cikin wani bidiyon, matashiyar ta kasance sanye da doguwar riga fara irin na amare a ranar aurensu, inda shi kuma angon ya sanya farin yadi dinkin babbar riga.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
Ekuaamoakowaa ya ce:
“Sashin bincikena na cewa ivy ifeoma da mijinta.”
Cee jay ta ce:
“Ke kadai ce…regina daniel da ivy ifeoma ne kawai za su iya ba ni shawara a duniyar nan.”
Yasmin Trunesh Hussein Ndiema ta ce:
“Duk mun yarda cewa imma dai hanyar Regina Daniels ko hanyar Kanayo .O Kanayo.”
HAWERO ya ce:
“Idan dai har kina cikin farin chomi.”
Jordan kudus ta ce:
“Ina girmama ka kudi.”
@preshchuks ta ce:
“Ke da Regina ne kawai za ku iya ba ni shawara a shekarar nan.”
Chachaluv ta ce:
“Ki bi kudi, soyayya za ta biyo baya na fahimce ki yar’uwa.”