Kannywood

Sarkin waka ya bayyana abinda yasa basa zama a inuwa daya da Rarara

Advertisment

A cikin shirin Gabon rooms talk show wanda take fira da fitattun jaruman masanantar kannywood a wannan sati kuma sarkin waka ya bayyana dalilin da yasa basa zama inuwa daya da Dauda Kahutu Rarara.

A cikin shirin anyi masa tambaya kamar haka:

Kana mawaki rarara yana mawaki amma miyasa baku zama inuwa da shi?

Sarkin waka Nazir M Ahmad yana cewa :

Advertisment

Nayi alkawalin bazan kara magana daga wannan akan dauda ba, abinda yasa nace daga wannan, wannan tambaya taki mai amfani ce duk wanda yace bama zama inuwa daya da dauda fada yake kawai shekara ta nawa ina waka shekarar shi nawa yana waka mun jima , kawai wannan zaben ne ya rabamu .

Ni anfiye ganina daman a inda ake gwagwarmaya inda ba gwamnati duk inda zanje akan buhari kadai shi kuma buhari mun dauko shi tin da, ni tun da nake shiyasa buhari nake yi har Allah yazo ya baiwa buhari har buhari ya gama mulki ae muna tare.”

Meyasa mutane ke cewa sarkin waka da rarara zama inuwa daya?

Idan baku manta wannan zaben da ya wuce sun ta muhawara da a kafafen sada zumunta wanda wasu mutane ke kallon tabbas babu jituwa tsakaninsu wasu kuma na kallon suna yuwa juna hassada ne, wasu na kallon sarkin waka yafi kudi ko a’a dauda rarara yafi kuɗi.

Sarkin waka yaci gaba da cewa.

Wannan siyasar da ta rabamu da ganduje da abba gida gida sai kuma wannan ta bola tinubu da wazirin adamawa so ina ji wannan sune kawai suka rabamu”

Ga bidiyon hirar nan .

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button