Labarai

Naji daɗin hukuncin da kotu tayi a kano – Dr. Idris Abdul’aziz dutse tanshi

Advertisment

A ranar labara ne dai kotun sauraren kararaki ta yanke hukuncin zaben Gwamna jihar Kano inda ta baiwa Dr. Nasiru yusuf gawuna nasara dan jam’iyar Apc wanda a halin yanzu Engr Abba kabir Yusuf dan jam’iyar NNPP ke rike da mulkin kano.

Dr. Idris Abdul’aziz dutse tashe yayi wannan maganar ne a bisa manbari inda yake nuna baiyi bakin ciki ba ga abinda yake fadi a cikin wani faifan bidiyo.

“Wannan abu da mutane kano sunka samu wannan bangare da musamman bangaren masu jar hula wallahi ni banyi bakin ciki ba kun san dalili basu da tarbiyya, Annabi s.a.w yace malamai magada annabawa amma ku kuma duk zagin ku, da rashin kunyar ku ,da sharrin ku sai yazo kan malamai.Naji daɗin hukuncin da kotu tayi a kano - Dr. Idris Abdul'aziz dutse tanshi

Wanda Manzon Allah s.a.w yace kifi da ke ruwa yana nema wa malami gafara in ya samu kuskure, kwari suna nema masa gafara, dabbobi suna nema masa gafara in yayi kuskure, mu ba ma’asumai bane, amma sai kasa samu fasiki, fajiri saboda siyasa dimokuraɗiyya kazo kana kana zagin malaminka.”

Advertisment

Dr. Idris tun kafin sati da za’a yanke hukuncin kotun yace yayi mafarki kotu ba baiwa yan bangaren can nasara ta kwace ga wancan, amma saboda mafarki ne ba komai yake yiyuwa ba sai gashi kuma abin ya kasance haka.

Malam ya kara da cewa

“To yanzu gashi din shugaban naku ya ɓalɓalce ba shugaban kasa, ba ministan , ba gwamnan ,ba siyasan to ina zai je, jam’iyar ma din sun kore shi to sai yah kuma.

Wai har yace in malami ya hau kan mambarinsa ya taɓa mu, muma zamu hau kan namu mambarin mu tura masha ashar, mu sa yara su zage shi, malamin zaka yiwa haka malami, ka taba jin kiristan ya taɓa zagin fasto ko raba ran faza su zage shi duk da suna da bambanci” inji shi malam

Ga bidiyon nan da yake fadi.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button