Mutumin Da Yabar Gida Kimanin Shekara Sama Da 50 tun Lokacin Faɗan Biafra ya Dawo Gida
Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Tudun-wada Hon. Ahmad Tijjani Musah (Matata), Shine Mutumin Da Ya Tashi Mota Daga Tudun-wada Kana Ya Haɗa Da Committee Daga Nan Tudun-wada Har Benue Domin Taho Da Malam Shu’aibu Kuma Alhamdulillah Suka Dawo Dashi Gida Ranar Alhamis.
Malam Shu’aibu Ya Faɗawa Chairman Baya Sallah, Baya Wani Addini Nan Take Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Tudun-wada Ya Bashi Kalmar Shahada.
Muna Yabawa Jami’an Sojoji Nigeria Da Suka Yaɗa Labarin Wannan Bawan Allah, Kana Muna Addu’ar Allah Ta’ala Ya Sakawa Mai Girma Chairman Bisa Kokarin Daya Nuna Na Dawo Da Malam Shu’aibu Gida Cikin Ƴan Uwansa Da Sauran Dukkanin Wanda Suka Bada Wata Gudunmawa, Amin Ya Allah .
Alhamdulillahi bada bata lokaci ba Shugaba karamar hukumar mulki Tudun Wada Hon. Ahmad Tijjani Musah ya bashi kalma shidda dalilin da yasa irin yadda ya dade a can yankin baya musulunci alhamdulillahi hon. Ahmad Tijjani ya umurni yan uwansa da limamai da a sama masa matar da zai aure da sauran abubuwa su kuma a gwamnatance zasu taimaka masa ga duk abinda ya sawwaka.
Yadda Sojoji Suka Gano Wani Mutumin Kano da Ya Bar Gida Tun Lokacin Yaƙin Bayafara Bai Koma Gida Ba
Malam Shu’aibu, mutumin Kano ne, ɗan asalin garin Tudun Wadan Dan Kade, ɗan gidan Mai Unguwa Tanko.
Ga asalin hirar da Ankayi da wannan bawan Allah yana cikin wani yanayi, amma alhamdulillahi yanzu ya iso gida.