Labarai

Maza: Shin ko kunsa abinda yasa Allah ya halicci ‘ya’yan maraina ? – Binciken masana

Advertisment

Albishirinku Ma’abota ziyarar wannan shafin mai albarka a yau munzo muku da sabon darasi na Dr.Umar Yamco matashin likitan nan mai amsa tambayoyin al’umma domin wayar da kansu, alhamdulillahi a wannan karo babin na maza ne idan kesan ke macece to ki ja jakarki ki wuce za’a fara bayyani dalla dallla.

“Da farko dai su ‘ya’yan maraina wasu kwallaye ne da Allah ya hallita a jikin kowa da namiji kuma Allah ya basu aiki ma muhimmin gaske a kowace rana suna kirkirar hallitar kwayoyin na ɗa namiji a turance “sperm cell” kenan wanda idan namiji ya sadu da mace guda daya akwai ake bukata sai a samu juna biyu.

Maza: Shin ko kunsa abinda yasa Allah ya halicci 'ya'yan maraina ? - Binciken masana
Maza: Shin ko kunsa abinda yasa Allah ya halicci ‘ya’yan maraina ? – Binciken masana

Hanyar da ake bi ana kirkira hallitar kwayoyin da namiji “sperm cell” kiran ana kiransa da suna da turanci ” spermatogenesis” ko wane zagaye ana gamashi ne baya kwana saba’in da hudu 74 .

Aiki na biyu : aiki da ‘ya’yan maraina suke yi shine suna kirkira wani abu da ake kira “testosterone” wannan wani abu ne da yake taimakawa maza wajen sha’awa kuma yana gina kashi, yana gina jiki kuma wajen kirkirar jini.

Abu na gaba shine kuma akwai wasu matsaloli wadanda ‘ya’yan maraina kan iya fuskanta.

Abu na farko shine “hydrocele” shine ruwa ya taru a wajen ‘ya’yan maraina din.

Abu na biyu shine “varicocele” shine kumburin jijiyoyin da suke dibar jini daga ‘ya’yan maraina zuwa zuciya.

Abu na ukku shine : inkwanal hainiya Sa’a nan akwai wata hanya da janyi zasu biyowa zuwa ya’yan maraina

Abu na hudu shine : akwai ” epididymis da “orchitis” wannan duk kumburi ne saboda kwayar cuta, za’a iya samun kumburi ko ƙari wanda yake iya zama kansa “Cancer”

Abu na biyar akwai : ” testicular torsion” wannan wani abun gagawa ne saboda murdewar jijiyoyin jini na marena.

Sa’a nan akwai ” cryptorchidism” wanda shine rashin saukowar ‘ya’yan maraina da ciki zuwa wannan yar jaka .

Shiyasa saboda wadandan yake da muhimmanci ɗa namiji yana duba ‘ya’yan marainansa ya din ga jin babu wani kumburi ko kari ga ya’yan marainansa.

Sai abu na karshe abinda yasa Allah ya halicci ‘ya’yan maraina a wata ‘ya jaka a wajen jiki shine ita wannan hanya da ake bi ana kirkira kwayoyin halittar da namiji wato ” sperm cell” wato “spermatogenesis” kenan hanye ce da bata so zafi kwata kwata wato zafin jiki zai iya kashe kwayoyin halitta Wato “sperm cell” kenan shiyasa Allah ya fito da su wajen jiki shiyasa saboda yana yin jikin mutum zai iya kashe kwayoyin halittar wato “sperm cell” kenan.

Abinda ake so a rike a nan shine ‘ya’yan maraina basa jin zafi shiyasa duk wata hanya da zata sanya ya’yan maraina daukar zafi ka gujeta .

Shine kamar zama a cikin ruwan zafi, ko kuma sa matsatson kaya wanda suke tattare maka ya’yan maraina naka haduwa da jikinka kenan. inji likita.

A nan darasin yazo karshe ga bidiyo nan ga mai son saurare.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button