Labarai

Mahaifi ya kashe jaririya kwana ɗaya da haihuwa saboda ya fi son ɗa namiji

Wani matashi dan shekara 28, mai suna Misbahu Salisu, ya kashe jaririyar da aka haifa masa, kwana ɗaya da haihuwa, saboda ya fi son ya samu da namiji jaridar daily Nigerian Hausa na ruwaito.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta kama mutumin da ke zaune a Doka Baici a karamar hukumar Tofa a ranar Juma’a.

Hukumar ta sanar da kama shi ne a cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan rundunar ɓangaren sintiri Mujahid Aminudeen ya fitar a Kano.

Aminudeen ya ce wanda ake zargin ya sanar da jami’an hukumar cewa ya bai wa jaririyar fiya-fiya shine ta rasu.

Salisu ya kuma baiwa mahaifiyar jaririyar mai suna Sa’ade kwaya a ciki shayi, inda bacci ya kwashe ta kafin ya aikata laifin.

“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fi son ɗa namiji ne amma matarsa ​​ta haifi mace, wanda hakan ya sa ya kashe jaririyar,” in ji jami’in a cikin sanarwar.

Ya ce an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button