Labarai

Magidanci ya kashe matarsa saboda Abinci

Yan sanda sun cafke wani magidanci da ake zargi ya kashe mai dakinsa saboda sabanin da suka samu a kan abinci a Jihar Edo.

Yan sanda sun cafke wani magidanci da ake zargi ya kashe mai dakinsa saboda sabanin da suka samu a kan abinci a Jihar Edo.

Rundunar yan sandan jihar ce ta gabatar da magidancin mai shekara 21 a yayin da take baje-kolin masu laifi da ke hannunta.

Jaridar watsa Aminiya Hausa na ruwaito wannan labarin Kakakin rundunar, Chidi Nwanbuzor, ya ce rundunar ta cafke wanda ake zargin ne bayan samun rahoton yadda ya jibgi matarsa da icen girki saboda sabanin da suka a kan abinci, har rai ya yi halinsa.

Daga baya ne yan sanda suke je wurin da abin ya faru a yankin Ugbekpe, suka dauke gawarta zuwa babban asibitin Fugar aka ajiye a mutuwari.

Shi kuma aka yi awon gaba da shi, domin amsa tambayoyi kan zargin aikata kisa.

Magidancin da ake zargin ya shaida wa ’yan jarida cewa rikicin ya samo asali ne bayan matar tasa ta dafa abinci amma ta hana shi.

“Ta dafa shinkafa ne amma ta hana ni, shi ne na dafa doya da kwai da kaina, amma shi ma ta ce ban isa in ci ba.

“Ina cikin ci ne muka fara hayaniya, ta yi barazanar kiran dan uwanta ya ba ni kashi. Na dauka barazana ce kawai, cani sai ’yan uwanta maza biyu suka zo kowanne dauke da sanda suka yi dambe da su.

Bayan fadan ne matata ta je gidan mahaifiyata ta kwana, amma washegari sai ’yan banda suka je suka kama ni, cewa na kashe matata,” in ji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button