Labari Mai daɗi: BUA ya fadi yadda zasu sayar da Siminti daga 4,500 a sabon farashi
Rabiu ya ce domin tallafa wa kokarin da gwamnati ke yi na sauƙaƙa farashin siminti, kamfanin BUA zai kara masana’antun yin siminti guda biyu a karshen shekara ko farkon shekara mai zuwa.
Shugaban BUA ya ce hakan zai ba kamfanin damar rage farashin simitin zuwa kusan N3,500 kan kowane buhu guda ɗaya. legit na ruwaito
Shugaban kamfin siminti Abdulsalam yana cewa:
“Bari na fara da gode wa shugaban ƙasa bisa karban bakunci na yau. Na zo ne domin tattauna wa da shi kan harkokin kasuwancin siminti. Muna da sabbin wurare biyu na tan miliyan 3 kowanne wanda zai fara aiki a ƙarshen shekara
Saboda haka na zo ne domin gana wa da shugaban ƙasa tare da bayyana masa irin kokarin da muke yi na marawa shirin gwamnati baya domin rage farashin siminti.” “Da wannan tan miliyan 6 da zamu kaddamar a ƙarshen shekara.
Kuma mai girma shugaban ƙasa ya amince zai kaddamar da masana’antun, wani lokaci a watan Disamba ko farkon Janairu na shekara mai zuwa.”
Da zaran mun kaddamar da wadannan wurare biyu kamfanin BUA Cement zai rika samar da kusan tan miliyan 17 a kowace shekara.” “Kuma da wannan ne muka kudiri aniyar sauko da farashin siminti daga farashin N5000 ko N5500 kan kowane buhu a yanzu zuwa buhu mai ƙila N3000 zuwa N3500.” “Kuma za mu iya yin hakan ne kawai saboda muna samar da siminti a cikin gida. Kashi 80% na albarkatun da muke amfani da su don samar da siminti suna cikin Najeriya.”
Wannan sanarwa ta fito jiya ne 15 ga watan Satumba a daidai lokacin da ya gama ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.