Kotu ta wanke wani barawon akuya shekara Daya Gidan Gyaran hali
Kotu a Kafanchan jihar Kaduna ta yanke wa Kefas Joshua hukuncin zama a gidan kaso bayan an kama shi da laifin satar akuya
Alkalin kotun George Gwani ya yanke wannan hukuncin ne bayan Joshua ya amsa laifin da ya aikata kuma ya nemi sassauci daga wurin alkali.
Jariar Premium Times Hausa na ruwaito alkali Gwani ya ce Joshua zai yi zaman gidan kaso na tsawon watanni shida bisa laifin shiga gidan mutane ba tare da izini ba ko Kuma ya biya tarar naira 5,000.
Ya kuma ce Joshua zai yi zaman kurkuku na tsawon shekara daya bisa laifin sace akuya ko ya biya tarar naira 20,000.
Bayan haka lauyan da ta shigar da karar Esther Bishen ta ce wani Sunday Biam ne ya ya kawo karar an sace masa akuya a ofishin ‘yan sanda ranar 3 ga Agusta.
Esther ta ce akuyar da Joshua ya sace za ta kai na Naira 60,000.
Ta ce ba tun yanzu ba ana yi wa Joshua shaidar sace sace a gari.