Labarai

Kotu ta tsare matar da aka kama tana madigo da ‘yar shekara 8

Kotun majistare dake Kafanchan jihar Kaduna ta daure wata mata mai suna Lois Iliya mai shekaru 36 kan laifin yin lalata da ‘yar shekara 8.

Jami’in rundunar Sibul Difens NSCDC Marcus Audu ya ce sun kama Lois ranar 13 ga Satumba bayan mahaifiyar yarinyar Alice Daniel ta Kai kara ofishin su.

Jaridar Premium Times Hausa na ruwaito, Audu ya ce mahaifiyar yarinyar ta ce Lois ta fara madigo da ‘yarta tun a watan Mayu ta hanyar lallabar yarinyar zuwa dakinta.

“Mahaifiyar ta ce Lois kan Saka yatsun ta a cikin gaban yarinyar kuma tana liliya nonon yarinyar da hakan ya sa nonon suka fara girma.

“Mahaifiyar yarinyar ta ce ta kai ‘yarta asibitin Salama inda likitoci suka tabbatar cewa ana lalata da ‘yarta.

Alkalin kotun Samson Kwasu ya ce za a daure Lois a kurkuku har sai kotun ta kammala yin shawara da fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar.

Kwasu ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 6 ga Oktoba.

Idan har an kama Lois da laifin madigo za a daureta na tsawon shekara 21 ga gidan Kaso.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button