Labarai

Kotu ta baiwa Al’ameen G-Fresh umurni yayi bikon matarsa sadiya haruna

A ranar 10 ga watan Oktoba ne wa’adin da kotu ta baiwa mawaƙi Abubakar Ibrahim (G-Fresh Al-amin) zai cika, na neman bikon matarsa Sadiya Haruna, wacce suka samu matsala yan kwanaki kaɗan bayan daura aure.

Lauyar G-Fresh, Barista Fatima Aliyu, ta ce wanda take karewa bai saki matarsa ba kuma bashi da niyyar sakin ta, saboda haka za suyi bikon ta kuma su na saka ran zasu cimma ƙudirinsu.

Kotun wacce ke zaune a filin Hockey dake Unguwar Hausawa ta amince da neman bikon ne bayan gaza samun sulhu da dukkan bangarorin su kayi a baya, wanda ɓangaren G-Fresh su kace sun nemi duk hanyoyin da zasu ga Sadiya amma abin ya ci tura, batun da bangaren Sadiya suka musanta.

Kuna ganin Sadiya zata amince da bikon kafin ranar 10 ga wata

Ga bidiyon nan.

Lauyar G-Fresh tace zasu cigaba da rarashin sadiya Haruna ganin an samu sulhu tsakaninta da mijinta domin su dawo su cigaba da zaman aure tunda soyayya ce ta hada su.

Lauyar ta kara da cewa abinda ita sadiya ta fadawa kotu shine bazata iya cigaba da zama da shi domin kuwa idan sunka cigaba zata iya saɓawa Ubangiji shine abinda ta fadi dalilin da ta ke so a raba auren.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button