Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano
Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Jaridar BBC Hausa na ruwaito.Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir, bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 18 ga watan Maris na 2023.
Kotun ta bayyana wannan hukunci ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro.
Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugabar kotun mai alƙalai guda uku.
Muna da tafe da ƙarin bayani