Kannywood

Hukumar tace fina finai , tana amfani da karfi kamar gwamnatin soja wajen ta-tsar kudade daga yan Kannywood da sunan sabunta rigista – Ty shaba

Jarumin kuma mai shirya fina finai a masana’antar Kannywood TY Shaban yace ba dai-dai bane a dinga karbar kudade daga hannun yan Kannywood da sunan sabunta rijista ba.

Shaba yace idan akayi la’akari da halin da kasa ke ciki na matsin tattalin arziki, bai dace hukumar tace fina finai da dab’i ta jihar Kano ta fito da tsarin kuntatawa yan masana’antar ta hanyar tatsar kudade daga hannunsu ba.

Acewar Shaba, kamata yayi hukumar tayi wasu gyare gyare da tsare tsare da zasu taimakawa masu shiryawa da masu bada umarni harma da jarumam masana’antar maimakon bigewa da karbar kudade daga hannun su hukumar tana tarawa kanta.

TY Shaban ya bayyana hakan ne a wani faifan video da ya wallafa a shafinsa na TikTok.

Mun samu labarin wanda da Sunkayi wannan rigista abun ya ninka sosai saɓanin na can baya abun yayi yawa fisabilillahi kowa yasan halin da Masana’atar nan take ciki, shi da kansa sabon shugaban ya fito da kansa yace shekara daya da wata tara babu fim daya da hukumar nan ta tace.

Ni naso ace abinda ya kamata miyasa fina finai nan babu su a yanzu , me zai kawo yadda za’a samu yan kasuwa masu zuba jari su cigaba da zuba jari domin farfado da wannan masanantar wane shawarwari za’a baiwa masu shirya finafinai nan domin dawo kama aiki gadan gadan.

Da yawa nasan furodusas da daraktas wadanda sun daina harka fim yanzu bazan kama suna ba domin tonon asiri ne amma yanzu bakin ka samu furodusas basu wuce mutum biyar masu shirya fina finai kam a Masana’atar wasu sunayi ne da ra’ayi an saba da riba ko babu riba.

Ga bidiyon nan domin karin bayani.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button