Hotuna : wata matashiya ta ƙyanƙyashe ƙwan da ta sayo a kasuwa
Zara, ‘yar shekara 13, ta ƙyanƙyashe ƙwayayen da ta sayo a kantin Sainsbury a wani tanki da take ajiye kunkuru tsawon mako uku, inda take jujjuya su sau huɗu a rana.
Jaridar BBC Hausa na wallafa a shafinta , daga bisani ƙwayayen sun ƙyanƙyashe salwa inda ta sanya wadda aka ƙyanƙyashe ranar Juma’a Pebbles sai kuma aka ƙyanƙyashe Speckles washe gari.
Mahaifiyar matashiyar mai suna Claire Sutcliffe ta ce: “Ba mu taɓa yarda hakan za ta iya yiwuwa ba. Abin ta’abiji ne.”
Zara, wadda ke yankin Altrincham na Greater Manchester, ta ce: “Na yi bincike sosai bayan na sayo ƙwan salwar guda biyu a kasuwa.”
Ta lura cewa ƙwayayen na iya ƙyanƙyashewa, sannan cikin tsanaki sai ta riƙa haska su da tocilan a lokacin da ta je juya su.
Mahaifiyar Zara ta ce ‘yar tata tana da son rayuwar dabbobi, kuma ta shafe tsawon watanni tana magana a kan batun. “Mu, ba mu ɗaukan hakan na iya yiwuwa ba. A ce an ƙyanƙyashe ƙwan salwa guda biyu, lallai wani al’amari ne.”
Sai dai, farin ciki da murnar da Zara ke yi, sun ragu, saboda ɗaya daga cikin ‘yan tsakin ya kamu da rashin lafiya.
“Ran Zara ya ɓaci kuma ta damu, inda ta ƙara sadaukar da lokaci wajen kula da Speckles,” a cewar Misis Sutcliffe.
“Daren jiya, barcin sa’a huɗu kawai ta yi, kuma ga shi za ta je makaranta da safiyar nan.
“Allah sarki, ɗan tsakon ba ya jin daɗi gaba ɗaya. Sai na ɗauke shi na kai shi asibiti, amma dai ba lallai ne ya rayu ba.”
Ƙwayayen salwa waɗanda ‘yan ƙanana ne, fiye da kima, ana ɗaukar su wani abincin daɗi a sassa daban-daban na duniya.