Hisbah ta kama Hadimin Sadiya Haruna, Sa’a nan GFresh ya bayyani matsayin auren su


Hukumar hisbah ta kano ta kama hadimin “P.A” din sadiya Haruna Abba Ado wayis akan rikicin su da Alameen GFresh inda yanzu haka dai shi P.A dinta abba yana a tsare wajen hukumar hisbah.
Sa’a nan zaku angon da ya bayyana matsayin aurensu da sadiya haruna gidan rediyon Freedom Radio kano sun kawo rahoto kamar haka.
Sayyada Sadiya Haruna ta bayyana cewa halin da ake ciki yanzu babu aure a tsakaninta da angonta, Al’ameen G-Fresh saboda ya sake ta tuntuni. “Ya sake ni tun a watan Ogas”. Ta ce.
Sadiya Haruna ta kuma ƙara da cewa G-Fresh ya buƙaci ta biya shi dukkan kuɗaɗensa da ya kashe wajen hidimar aurenta kuma ta ba shi.
Sai dai kuma, a nasa ɓangaren, Al-Ameen ya bayyana cewa atafau fa shi bai saki matarsa ba, akwai aure a tsakaninsu wani ne dai da ke zaman P.A ɗinta abba ado wayis ya ke hure mata kunne domin har abinci su ke ci tare shi kuma a matsayinsa na mijinta ta zuba mas a wani kwanon daban.
Shin ko minene alaƙarki da Abba Ado wayis?
“Abba P.A na ne a gidansu abba mahaifiyarsa da yayansa babu wanda bai san ni ba, kuma yasan matsayinsa a gurina kuma abba ne yake min transfer komai da komai dina koda bana gari irin nayi tafiya misali irin na tafi Saudiya. Inji sadiya haruna”
Shin da gaske ka saki matar ka sadiya Haruna?
“Ko da wasa ban saki matata ba auren soyayya mu ka yi, saboda sonta da nake yi shiyasa na aureta, sai dai idan ita take da wata manufa amma ni tsakanina da Allah na aureta, burin in zauna da ita.
Wasu mutane na cewa banda sirri to ae itace ta fara chichilo habaici a soshiyal midiya.”
Sadiya haruna ta bayyana cewa ita babu aure tsakanin ta da Alameen GFresh tun watan ogas ta ta hanyar lauyan ta ga yadda tayi bayyani dalla dalla
“Ni babu aure tsakani na da shi, saboda a lokacin da munka samu sabani da shi ni in bashi kudinsa ya gaji da zama da ni, sai nace wane kudi kake bukata wanda ka kashe a hidimar auren mu, wanda ba lefe kayi ba daga sadaki sai sadaki , sai yace shi na dauki kudinsa na bashi .
Da bakinsa ya furta ya sake ni ya dauki fansa ya bar gidana yace ni na kore shi , to haka na tafi saudiya sai na bude soshiyal midiya naga mutane suna ta tsine mun, shima ya tara mutane a live na tiktok kenan ana cewa ina yawo da aurena inji ta.
ta ƙara da cewa Kotun da na kai shi ba wai dan na kai shi kotu ba ne don na wulakanta shi ba ko nayi rikici da shi ba a’a, na kai shi kotu ne domin tayimin iya ka da shi ne Sa’a nan ya kara rubuta takarda a rubuce – inji sadiya Haruna.
Ga rahoton nan.
Yanzu dai kallo ya koma sama a hisbah yadda za’a warware wannan dambarwa .