Labarai

Gwamnan Kebbi ya naɗa dan gidan Sheikh Giro a matsayin mamba a kwamitin gudanarwar hukumar alhazai

Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya nada Hussaini Abubakar Giro a matsayin mamba a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, domin maye gurbin mahaifinsa, Sheik Abubakar Giro, wanda ya rasu a ranar Laraba.

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’iqamatus Sunnah ta kasa, JIBWIS, a baya ta roki gwamnan da ya duba daya daga cikin ‘ya’yan marigayin domin bashi mukamin da aka bai wa mahaifinsu, inda gwamnan ya amince.

Ahmed Idris, mai magana da yawun gwamnan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Birnin Kebbi a yau Lahadi.

Gwamnan Kebbi ya naɗa dan gidan Sheikh Giro a matsayin mamba a kwamitin gudanarwar hukumar alhazai
Gwamnan Kebbi ya naɗa dan gidan Sheikh Giro a matsayin mamba a kwamitin gudanarwar hukumar alhazai

Idris ya ruwaito gwamnan na bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar, a karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Sheik Abdullahi Bala-Lau, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.

Gwamnan ya tabbatar wa kungiyar cewa an riga an amince da bukatar ta su.

Idris ya gode wa kungiyar bisa wannan ziyarar, yana mai cewa: “Rashin ba ga iyalansa kadai ba ne, har ma ga dukkanmu.”

Tun da fari, shugaban JIBWIS din na kasa ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin rashi ba ga jihar Kebbi kadai ba har ma da Najeriya da Afirka da sauran al’ummar musulmi baki daya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button