Faransa ta tura dakarunta kasashen ECOWAS don shirin kai wa Nijar hari – Sojoji
Sojojin na Nijar sun kara da cewa ranar 7 ga watan Satumba wani jirgin ruwan yakin Faransa ya isa Cotonou babban birnin Benin dauke da dakaru da ke shirin kai musu hari.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli sun yi zargin cewa Faransa tana tura sojojinta zuwa kasashen Yammacin Afirka da dama da zummar yin amfani da “kafin soji” a kansu.
“Faransa tana ci gaba da kai dakarunta kasashen kungiyar ECOWAS da dama a wani bangare na shirin kaddamar da hare-hare kan Nijar, wanda take kitsawa tare da hadin gwiwar kungiyar,” a cewar kakakin sojojin Kanar Amadou Abdramane a wata sanarwar da ya karanta a gidan talabijin na kasar ranar Asabar da maraice.
Babba jaridar watsa labarai TRTAFRIKA Hausa na ruwaito wannan labari ya ce Faransa ta tura dakarunta kasashen da suka hada da Senegal, Benin da Ivory Coast, a wani bangare na ”shirin kaddamar da hari” a kan Nijar.
Kawo yanzu dai Faransa ba ta yi martani kan wanna zargi ba.
Amma Kanar Abdramane ya yi ikirarin cewa ranar 1 ga watan Satumba Faransa ta tura jiragen soji biyu da kuma wani jirgi samfurin Dornier 328 domin karfafa dakarunta da ke Ivory Coast, yayin da kuma ta tura jiragen helikwafta biyu samfurin PUMA da motoci masu silke 40 zuwa Benin.
Ya kara da cewa ranar 7 ga watan Satumba wani jirgin ruwan yakin Faransa ya isa Cotonou babban birnin Benin dauke da dakaru.
Ranar Litinin Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce sojojin suna tattaunawa da Faransa da zummar tabbatar da “gaggawar” kwashe dakarunta daga kasar.
Sai dai sojojin sun zargi Faransa da “rashin gaskiya da jan-kafa da kuma kafar-ungulu” don kawai ta kawar da su.
Dangantaka tsakanin Faransa da Nijar ta yi tsami bayan Paris ta dage cewa dole sojoji su mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki bayan juyin mukin da suka yi masa ranar 26 ga watan Yuli.
Juyin mulkin ya sa kungiyar ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumai sannan ta yi barazanar amfani da karfin soji idan aka gaza cimma matsayar mayar da Bazoum kan mulki ta hanyar diflomasiyya.
Faransa tana da dakaru sama da 1,500 a Nijar wadanda suke hadin-gwiwa wajen yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, sai dai sojojin kasar sun soke dangantakar da ke tsakaninsu da kasar tun bayan juyin mulki.
Hasalima sun umarci jakadan Faransa ya fita daga Jamhuriyar Nijar, ko da yake har yanzu yana kasar.
Dubban mutane ne suka rika gudanar da zanga-zangar kin jinin Faransa a Yamai, inda suka bukaci kasar ta.
Mawallafa: TRTAFRIKA HAUSA