Ciki ne da ni na wata takwas (8) kuma ina so in zubar – labari daga asibiti


Wani likita mai suna pharm.Musa A.bello da yake aiki a asibiti ya kawo wani labari mai ban tsoro a wannan rayuwa inda yake cewa wata matar aure ce tazo tana son zubar da cikin da take dauke da ita na wata takwas (8) ga yadda labarin yake.
Ciki ne dani wata takwas kuma zan zubar wannan shine furucin da wata mata tayi lokacin da taje famasano, wannan labarin inaso in bayar da shi ne saboda mutane su dau darasi na rayuwa.
A lokacin na fahimci a kudurin ta lallai sai ta zubar da cikin nan,saboda in banda haka da cewa zanyi ki fice daga nan mu nan bama zubar da ciki a nan bamu sam me hakan yake nufi ba, to amma akwai wani darasi a harka lafiya muna karatun “psychology” karanta yanayin rayuwar dan adam da tunaninsa da sauran abubuwa.
Likitan yace ta shigo da sunka tsaya suna magana sai take gayamasa cewa sunyi fada da mijinta ne tana so ta zubar da wannan cikin na wata takwas ta raba duk wata alaƙa da take tsakaninta da shi, a nan ne likitan yace wannan abun ba a nan take yake yiyuwa ba hajiya, tace wannan ba damuwar ta bane ko nawa zata kashe, kai in kare muku nan take ta cire yan sababbin naira dubu dubu bandir daya dubu dari kenan 100k.
Nace hajiya baki gane ba tace fadamin account number dinka domin na fahimci muhimmancin abinda ke kasa, a nan na fahimci cewa tabbas wannan matar idan har na bari ta fita zata je inda wasu zasu karbi kuɗin suyi mata, tunda akwai wandanda basu tsoron Allah.
Nace to wnanan abun ba kai tsaye za’a yi miki ba saboda zai iya sanadiyar rashin lafiyar ki sai tace ita bata damu ba, sai nace to zai iya sanadiyar rayuwarki.
Ga bidiyon nan ku saurara kuji yadda abun ya kasance.