Ban taɓa samun namijin da ya ɗanɗana min ɗan soyayya kamar Dr. sheriff Almuhajir – inji murya kunya
Fitacciyar jaruma a shafin Tik-Tok Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewa ba ta taɓa sanin daɗin soyayya ba sai da ta haɗu da Shehin Malami Dakta Sharif Al-Muhajir. “Ban taɓa samun namijin da ya ɗanɗana min daɗin soyayya kamar Dakta Sharif Al-Muhajir ba. Ban taɓa sanin cewa zan haɗu da mutum mai kima da daraja irinsa a rayuwata ba”. Cewar Murja Kunya.
Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito haka bayan da Dr. Al-Muhajir ɗin ya gana da murja inda ya bayyana cewa: “ashe haka Murja Kunya ta ke yarinya mai hankali da nutsuwa, Masha Allah. Gaskiya kar ku yi mamakin ganin sunan almajiri a list din auren zawarawan Kano”. A shafinsa na Facebook.
A nata ɓangaren, Murja Kunya ta ƙara da cewa a matsayin Dr. Al-Muhajir na mutum mai addini da ilimin zamani da wayewa da rayuwa, a shirye take ko da mako mai zuwa a ɗaura musu aure ta yarda.
Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan da gwamnan Kano, Eng. Abba K. Yusuf ya bayyana cewa Murja ƴar’uwarsu ce da ke ba wa gwamnatinsu gudunmawa saboda haka ta nemo miji a sanya ta cikin shirin auren zawarawa.