Labarai

Babban Dan Shugaba Tinubu Seyi Ya Bada Miliyan 15 Ga Iyalin Mawaki Mohbad

Dan shugaban kasa Bola Tinubu, Seyi, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 15 ga Liam Aloba, dan marigayi mawakin Najeriya, ‘Mohbad.

Mataimaki na musamman kan shafukan sada zumunta ga shugaban kasa, Olusegun Dada ne ya bayar da tallafin ga jama’a a kan X (wanda aka fi sani da Twitter) jaridar dimokuraɗiyyar na ruwaito.Babban Dan Shugaba Tinubu Seyi Ya Bada Miliyan 15 Ga Iyalin Mawaki Mohbad

Dada wanda ya raba takardar hada-hadar kudi ta N15m a hannunsa, ya jinjina wa Seyi Tinubu kan gudummawar da ya bayar, inda ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya gaji ubansa a fannin kyautatawa da kuma jinkai.

Wannan alƙawarin yana nuna ƙudurin dangin Tinubu na tallafa wa haziƙai a cikin masana’antar kiɗan Najeriya musamman wadanda suka rasa rayukansu inji Dada.

A cewar Dada, shi ma ya shiga cikin makokin Mohbad wanda ya mutu a wani yanayi mai sarkakiya

Sakon Dada ba wai kawai ya nuna irin gudummawar da Seyi Tinubu ya bayar ba amma kuma ya jaddada tasirin goyon bayan da dangin Tinubu ke ci gaba da yi ga hazikan mutane a masana’antar waka ta Najeriya.

Mohbad wanda ya mutu a cikin yanayi mai cike da cece-kuce yana samun ta’aziyya da yabo daga magoya baya da sauran masu fasaha baki daya.

Mutuwar tasa ta bar baya da kura a masana’antar waka, wanda hakan ke tunatar da mu irin raunin rayuwa da kuma muhimmancin tallafawa da kuma renon hazikan matasa.

Yan sandan Najeriya dai sunsha alwashin yin kwakkwaran bincike akan mutuwar da Mohbad wanda ya mutu ba tare da an san ainahin abinda ya zama sanadiyar rasa ransa ba.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button