Labarai

Ba ni na kashe Mohbad ba – Naira Marley

Ni ba ɗan ƙwaya ba ne - Naira Marley

Mawaƙin Najeriya, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley ya sake jaddada iƙirarinsa na cewa ba shi da hannu a kisan tsohon abokin aikinsa, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da daddare, Naira Marley ya ce, kamar kowa, shi ma ya shiga cikin damuwa sosai sanadiyyar mutuwar tsohon yaron aikin nasa.

Naira Marley ya ce Mohbad ya bar kamfanin ‘Marlian Music’ ne a watan Satumban 2022, sai dai ya ƙara da cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu ba ta kai yadda ɗaya daga cikin su zai riƙa yi wa ɗan’uwansa fatan mutuwa ba.jaridar Bbchausa na ruwaito

“Gaskiya ne cewa mun samu saɓanin fahimta a lokacin da muke aiki tare, amma saɓanin bai kai yadda mutane ke zuzutawa ba. Bai kai yadda za mu yi wa juna fatan mutuwa ba.” In ji Naira Marley.

Ya kuma ce sun riƙa ƙoƙarin warware rashin jituwar ta hanyar shari’a gabanin mutuwar Mohbad.

Marley ya ce dalilin da ya sa ya yi gum da bakinsa game da mutuwar ta Mohbad shi ne saboda kaɗuwar da ya yi, da kuma gudun kada ya kawo cikas ga binciken da jami’an tsaro ke yi kan mutuwar.

Ba ni na kashe Mohbad ba - Naira Marley
Ba ni na kashe Mohbad ba – Naira Marley Hoto/BBCHausa

Ya kuma ƙara da cewa ya bar Najeriya ne tun a ranar 31 ga watan Agusta, kuma bai dawo ba tun wancan lokacin, sai dai yanzu haka yana shirye-shiryen dawowa domin amsa gayyatar ƴan sanda.

‘Ni ba ɗan ƙwaya ko ƙungiyar asiri ba ne’

Naira Marley ya kuma ce kamfaninsa ba cibiyar ta’ammuli da ƙwayoyi ko ƙungiyar asiri ba ne. Inda ya ce shi kansa ba mai safarar ƙwaya ko ɗan ƙungiyar asiri ba ne.

Ya ce “Marlian Music kamfani ne na wasu aminan juna, waɗanda ke gudanar da ayyukansu ta halastacciyar hanya. Manufarmu ita ce yin jagora ga mutane masu basira da tallafa musu.”

A ranar 12 ga watan Satumba ne Mohbad, mai shekaru 27 a duniya ya rasu, inda yanzu haka jami’an hukumar tsaro ta DSS ke gudanar da bincike kan mutuwar tasa.

Lamarin ya kai ga cewa an sake tono gawar mamacin bayan binne ta domin gudanar da bincike, inda yanzu haka ake jiran sakamako.

Mutuwar Mohbad ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya da ƙasashe maƙwafta, musamman a shafukan sada zumunta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button