Labarai

An yi zanga-zangar kyamar Faransa a Vienna kan haramta sanya abaya

Wasu masu zanga-zanga sun taru a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Vienna don bayyana adawarsu da matakin da hukumomin Paris suka dauka na haramta sanya abaya a makarantu.

Masu zanga-zangar sun sanya abaya kuma suna dauke da kwalayen da aka rubuta “sanya abaya ‘yancinmu ne kuma asalinmu ne”, “Ni nake da zabin tufafin da zan sanya, ba wani ba” da makamantansu.

Ana kallon wannan mataki a matsayin nuna kyama ga mata Musulmai da ke kasar.

Jaridar TRTAFRIKA na ruwaito Daya daga cikin masu zanga-zangar ita ce Baraa Bolat, wadda ke da dimbin mabiya a soshiyal midiya saboda fafutukar da take yi wajen kare hakkin dan’adam.

“Ni da sauran mutane muna kallon wannan mataki a matsayin wulakanci ga jama’a. Bai kamata a yi irin wannan shirme ba,” in ji Bolat a hirarta da kamfanin dillancin labaran Anadolu.

“Ya kamata a bai wa mata damar sanya tufafin da suke so. Ni da sauran mutane muna ganin ya kamata a ce mace ce za ta zabi ta sanya abaya ko kuma siket. Wannan mataki ne da mace ya kamata ta yanke hukunci a kai ba wani ba.”

Bolat ta ce sun gudanar da zanga-zangar ce domin jan hankali kan batutuwan da ba a mayar da hankali a kansu da kuma kyamar matakin Faransa na haramta sanya abaya.

 

“Ba ma so a dauki irin wannan mataki a wasu wurare ko kuma a haramta sanya wannan tufafi a Austria da ma wasu kasashe. Wannan take hakkin mutane ne. Bai kamata gwamnati ta gaya wa mutane irin tufafin da za su sanya ba. Hakan ne ya sa muke gangami mai taken ‘zabina ne sanya tufafin da nake so, kuma zabina ne sanya abaya.”

Take hakkin Musulmai

A farkon watan nan ne Ministan Ilimi a Faransa ya haramta wa mata sanya abaya a makarantu yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasar na “raba addini da lamuran hukuma.”

Ministan Ilimi Gabriel Attal ya ce dalibai kusan 300 ne suka bijire wa dokar haramta sanya abaya kuma an kore su gida — a ranar farko da aka koma makaranta bayan hutu.

Yawancinsu sun amince su sauya tufafin da ke jikinsu amma 67 sun ki yarda su cire abaya, kuma an kore su gida, a cewar ministan.

Matakin ya faranta ran masu tsattsauran ra’ayi amma masu sasaucin ra’ayi sun ce hakan take hakkin mata Musulmai ne.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button