Labarai

Kotu ta yanke wa mahaifin da ya yi shekara 9 yana lalata da ƴa’ƴan sa mata biyu

Kotun dake sauraron kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ta yanke hukuncin daurin rai da rai wa Eze Chukwuma mai shekara 59 bayan an kama shi da laifin yi wa ‘ya’yan sa mata fyade.

Lauyan da ta shigar da karar Olufunke Adegoke ta ce Chukwuma ya fara yi wa ‘ya’yan sa fyade daga shekarar 2008 zuwa 2017 a gidan su dake lamba 2 layin Agbeke a Iyana-Era Bus Stop, Ijanikin.

Jaridar Premium Times Hausa na Adegoke ta ce a lokacin matarsa kuma mahaifiyar yaran ta mutu wajen haihuwa.

“A lokacin da Chukwuma ya fara lalata da yaran babban ‘yarsa na da shekara 9.

“An kai yaran kauyen su inda a nan yaran suka bayyana ta’asar da mahaifinsu ya riƙa yi da su amma babu matakin da aka dauka.

“Bayan sun dawo Legas ne babban ‘yar ta gudu sannan ita karamar ta kai karar abin dake faruwa da ita a makaranta inda daga nan makarantar sanar da ma’aikatar ilimi.

A kotun Chukwuma ya amsa laifin da ya aikata sannan ya nemi a yi masa afuwa.

Zuwa yanzu ‘ya’yan Chukwuma na zama a gidan marayu dake jihar Legas.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button