Labarai

Wace ce Maryam Shettima? Minister A Gwamnatin Tinubu

Dakta Maryam Ibrahim Shettima
DPT (BUK), Msc (University of East London), Kingian Fellowship (Emory University Atlanta USA)

Dakta Maryam Ibrahim Shettima, (wadda aka fi sani da Maryam Shetty), ‘yar siyasa ce, mai fafutukar ci gaban al’umma sannan kwararriyar likitar kashi ce wadda tayi aiki a wurare daban-daban.

Tayi digirin ta na farko a jami’ar Bayero dake Kano sannan ta samu digirin ta na biyu a jami’ar Stratford dake burtaniya inda ta karanta fannin kula da kashi na bangaren wasanni.

Tana daya daga cikin likitocin da suka tafi da tawagar Nigeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin London din kasar Ingila a shekara ta 2012 inda tayi aiki tare da manya-manyan ‘yan wasa da suka hada da shahararren dan wasan tseren nan dan kasar Jamaica, Usain Bolt, da sauran zakakuran ‘yan wasan da suka halarci gasar a shekarar.

Har ila yau, Dr. Maryam Shetty, ta samu shaidar kwarewa ta yaki da rikice-rikice da taimakon gidauniyar Dr. Martin Luther King Jr a jami’ar Emory dake kasar Amurka sannan ta samu shaidar kwarewa ta ”kalubalen samar da manufofi domin al’umma a jami’ar Virginia itama dake kasar Amurka.Wace ce Maryam Shettima? Minister A Gwamnatin Tinubu

Tana da kwarewa sosai wajen yin aiki a cikin gida da kungiyoyi da cibiyoyi na kasashen waje inda a baya ma tayi aiki da gidauniyar tallafawa al’umma ta burtaniya, sannan tayi aiki a asibitin fadar shugaban kasa dake Villa da cibiyoyin kula da lafiyar yara na duniya.

Bugu da kari, Dr. Maryam Shetty sananniya ce wajen fito da tsare-tsaren tallafawa al’umma musamman a bangaren ci gaban ilimi inda ita ce ta jagoranci Shirin gyaran makarantu a jihar da ta fito, wato jihar Kano a karkashin Shirin nan na “tallafawa inda ka fito”

Saboda kokarin ta da sadaukarwar ta wajen kishin kasa da ganin al’umma ta samu ci gaba, ta samu damar wakiltar Nigeriya a babban taron majalisar dinkin duniya na shekarar data gabata akan “tabbatar da gaskiya da adalci da kuma yaki da cin hanci da rashawa”

Maryam Shettima ta samu digirin girmamawa sakamakon jajircewa da kokarin ganin suma al’umma an tafi dasu domin samun ci gaba daga jami’ar fasaha ta ESGT dake jamhuriyar Benin.

A siyasance, Maryam Shetty ta bayar da gudunmawa wajen fita yakin neman zaben shugaban kasa. Sannan jigo ce a cikin kwamitin matasa da mata na yakin neman zaben shugaban kasa, sannan tana cikin kwamitin tsarawa da yada labarai, har ila yau tana cikin wakilan jam’iyyar APC mutum 7 da suka jagoranci ganin anyi zaben jihar Delta cikin kwanciyar hankali.

A matsayinta na jigo a cikin jam’iyyar APC, tana cikin manyan mata daga yankin arewa da suka tsaya tsayin daka wajen yakin neman zaben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima. Sannan ta taka muhimmiyar rawa wajen zaben fid da gwani na zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC wanda shugaba Bola Tinubu ya samu nasara.

Dr. Maryam Shettima ta ci gaba da yin kira domin ganin an samu zaman lafiya da shugabanci na gari da kuma ganin an ci gaba da shigar da mata da matasa wajen damawa a harkokin ci gaba ta hanyar tsarin nan nata tilo da aka santa dashi na “Webelieve”

Idan ana maganar zamantakewa kuma Dr. Maryam Shettima sananniya ce wajen ganin al’umma sun zauna lafiya tare da samar da yanayin da kowa zai zauna lafiya da dan uwansa.

Sannan mace ce mai ganin girman mutane, babba da yaro, tana da kishin al’ummar ta, har ila yau, tana kokarin ganin ta tallafawa al’ummar ta idan har ta samu wata dama domin kuwa akwai mutanen da dama itace sanadiyyar sama musu aiki.

Tana da kishin Nigeriya da inda ta fito, kuma tana da kishin al’adar ta, addinin ta da al’ummar data fito, sannan bata fada da mutane domin zaiyi wahala kaga ance ga wani wanda suka samu rashin jituwa da ita.

Rubutawa: Rukayyat sadauki

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA