Tabdi Jam: Adam Zango na neman kira wa kansa ruwa garin yin turanci ya jawo cece kuce


Kodayake dai ilimi kogi ne, to amma ga dukkan alamu Jarumin Kannywood Adam A. Zango ya saka kansa tsaka mai wuya sakamakon wani rubutu da yayi a shafinsa na sadarwa zamani da ya jawo cece-kuce da muhawara mai zafi, domin ana ganin kalaman sabo ne karara
Adam a zango ya dauko wata karin magana ce ta wani bature dake cewa
“Being perfectly well-dressed gives one a tranquility that no religion can bestow.”.


To sai dai bisa dukkan alamu jarumin bai natsu ya duba fassarar wannan magana ba fitaccen marubuci mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook Dr. Abdulaziz T. Bako yayi fasarar wannan rubutun a sauke ga abinda yake rubutawa.
“Manta da kura-kuran turanci da ke cikin maganar.
Maanar shine sanya sutura ta gani ta fada ya fi duk wani abu dangin addini baiwa zuciya kwanciyar hankali.
A saukake: sutura mai kyau ta fi sallah (ga musulmi)ko zuwa coci (ga kirista) baiwa zuciya natsuwa.
Don Allah a turawa Adam zango wannan fassarar.”
Wannan rubutu ya jawo dubban muhawara har wasu ke yin kira ga jarumin ko dai ya gyara rubutun ko kuma ya cire shi domin sabo ne karara, sannan uwa uba baturen da yayi maganar babban fegan ne wato wadanda basu yarda da addini ba
To sai dai ana sauraron Jarumin ya yiwa jama’a karin haske kan abunda yake nufi da wadannan kalamai nasa da suka jawo Allah-wadai .
Hausaloaded ta samu tattaro muku kadan daga cikin martanin mutane akan wannan rubutu.
@Abba Yakasai cewa yake: Na rantse da Allah Dr da yawan masu mocking dinshi idan Banda yanzu ka fassara zuwa Hausa wlh basusan Mai yake nufi ba suma..
@Kabiru s. bako cewa yake :
Matsalar shine kila ma plagiarizing yayi, ana matsawa zai bara. Allah ya kyauta.
@muhamad Nasir Rida cewa yake :
Amma ka san miye tranquility din kuwa ko dai mu zo mu fassara maka?
To yanzu rigar ta ka ta fi ba ka nutsuwa akan addini kenan fa. Idan aka matsa sai kalaman su zama ridda fa
@Atikatu Ibrahim cewa takw :
Shifa Adam zango Bai iya turanci ba ko da akai hira dashi yace burinsa y iya turanci. Yana Dan ganewa ne kadan kadan wlhy shikansa nasan baisan fassarar abinda yarubuta ba fassarar en koyo yaywa turancin. And mutane sunce copy and paste yayima Dan iskanci .
@ahmad Muhammad cewa yake:
To yanzu Ina matsayi wanyanda suka ce Masa Masha Allah yake acikin comments section dinsa yake yanzu,Nifa in ban iya abuba kwata kwata banayi Sabo da zaman lafiyata kanayimin magana da turanci zance maka in bakajin Hausa Kaware kawai shine Gaskiyar Batu.
@Aliyu Samba cewa yake : Haba Likita, kaima har da kai. Wannan fa quote ne daga Ralph Waldo Emerson kuma he is a poet. Ba zai yiwu a bawa irin wannan zantukan fassara ta kai tsaye haka ba.
Kaman nine na zo ina bayanin karfin mutum a matsayi poet, sai nace;
“Idan yayi kunji, rugugin sautin sa na hana girgije kwararo da ruwa”
Shin hakan sai ya zama ina nufin a zahiri in yayi tsawa ya a dakatar da girgije daga zubda ruwa?.
@Abdulaziz T. Bako cewa yake : Aliyu Samba wannan quote ne da ake amfani da shi frequently a advertisements na kayan sakawa don a nunawa mutane muhimmancin sutura, wanda hakan yana nufin cewa abinda ake nufi kenan cewa kayan sakawa suna baiwa zuciya nutsuwar da addini bai isa ya iya bata ba..
@yakubu musa cewa yake: Abdulaziz T. Bako Kafurci ne tsantsa. Ai ba excuse. Shi yasa na ce Zango bai nemi google translate ba