Sojoji sun samu nasarar karbo mutune 9 daga yan ƴan bindiga a Zamfara


Yanzu nan majiyarmu ta hausaloaded ta samu wani labari mai dadi wanda tabbas wannan abin aya bane wanda hukumar sojoji sunkayi kamar yadda shafin maibiredi tv sunka ruwaito.
Sojoji sun samu nasarar karbo mutane 9 ‘yan asalin jahar Sokoto da aka yi garkuwa dasu a ta cikin kauyen Gadar zaima ta jihar Zamfara.
A lokacin bata wuta da akayi, Sojojin sun samu nasarar kàshe ‘yan bindiga 10 tare da ràunata wasu da-dama.
Sojojin kuma sun kama mutane 2 cikin ‘yan bindigar, tare da Bindigogi shida kirar AK-47, Bindiga 1 kirar 1PKT da kuma Magazine 5. Sauran su ne harsasai 7.62MM mai rawun 20, wayoyin hannu 3, Fanel din Sola 2, Keken Dunki (Tela) da Naira Miliyan 2,410,000.
‘yan bindigar sun samu nasarar kàshe wata Mace cikin mutane tara da aka kwato a lokacin da suke bata kashi da Sojojin.
Allah ya kawo muna zaman Lafiya Mai dorewa.