Labarai

Rayuwa ta da Mijina ta Fannin Gaisuwa Da Kulawa – Hajiya Fatima chikaire

Advertisment

Zanyi sharing wani fanni na rayuwata da mijina da ya danganci gaisuwa da nuna kulawa, ba dan komi ba sai dan ina son mu fahimci yanayin yadda kowa ya dauketa ko ya ke yinta.

1st shekarun da ke tsakanina da mijina dai shekara goma sha ɗaya (11) ya ke bani, shekarun auren mu kuwa kusan 21 muke nema yanzu.

Rayuwa ta da Mijina ta Fannin Gaisuwa Da Kulawa  - Hajiya Fatima chikaire
Rayuwa ta da Mijina ta Fannin Gaisuwa Da Kulawa – Hajiya Fatima chikaire Hoto:. Fatima chikaire

Amma duk wayewar gari sai na gaishe shi, in a waya ne, ko in ya dawo gida. Nakan masa nau’i 3 na gaisuwa wadda ko wanne da yanayi, lokaci da dalilin da nakeyi.

1. Nakan masa gaisuwa ta girmamawa wadda har qasa nake sa guiwowina kafun in gaishe shi, ko in masa gaisuwar ‘yar duƙawa na rage tsawo( in ya dawo daga office)
2. Na kan masa gaisuwa irin ta qauna wadda ya shafi gaisuwana kalamai dake haɗe da hugs da kisses
3. Nakan masa gaisuwa irin ta aboki, mu sha hannu mu ware.

Ko a waya na kirashi ko ya kira sai na tabbata na masa gaisuwa da sanin yanayi da lafiyar sa.

Duk da kasancewar sa shugaba na, amma yakan gaishe ni wadda yakan bayya a cikin nau’i biyu :
1. Gaisuwa na ƙauna da tausayi
2. Gaisuwa irin ta abokai.

Duk randa ya rigani tashi zanji yana “good morning”, “good morning” ko good morning beautiful” tashi kar inyi letti, zai hada da hugs and kisses wannan al’adace da muka jima da sabarma kan mu.

In kuwa dawowa gida yayi daga office mukan tarbi juna da hugs and kisses ( sai in daya ko dukan mu da alwala tare da mu) haɗi da faɗin “good to see you” “good to see you too”. Muna idar da wannan sallar da muka riqema wannan alwala zamu yi gaisuwa ta soyayya da muka sabarma juna.

In kuwa yayi baƙi suka jima suna palour bai ji ɗuriyata ba (kasancewar yasan nakan so zama da hira dashi), zai bar abokan sa ya shigo in da nake ya na zuwa zaice “naji ki shuru ne nace barin zo in gaishe ki” nakan ce masa “godiya nake da wannan gaisuwa” . Hakan da yake yakan sa naji daɗi dan yakan tunani duk da yana cikin nishaɗi da abokan sa.

Farkon azumi mukan raba ɗaki dan lokacin bacci da tashin mu ya kan banbanta sosai, so nakan rigashi bacci da tashi dan shi yana da abokan shan ruwa kuma sukan tsaya dan hira kafun su tafi, ni kuwa ina gama Asham nake bacci.

Amma baya taɓa wucewa ba tare da ya shiga ya dubani ba, ko nayi bacci ko banyi ba zai shigo ya dubani, in ya tashi tahajjud duk da nakan riga shi tashi, amma kafun ya soma zai zo ya dubani dan tabbatar da na tashi, in kuwa naji shi shuru nakanje in dubashi dan nasan ya makara wajen tashi.

In ban da lafiya ban cika kwana in da yake ba dan kar zafin jikina da yawan motsi ya hanashi bacci, amma duk dare zai shigo ya dubani sau biyu dan tabbatar da lafiya da yanayin da nake ciki, wani lokaci bana ma sanin ya shigo sai dai yace na dawo naji kin samu bacci lokaci kaza

Wani lokaci kuwa in na gaidashi yakan ce min bazai amsaba sai na tsuguna kafun ya amsa, nan take ba musu nakan tsuguna har ƙasa in sauya yanayin kalamaina wadda nakan dawo dashi na saurata, isa da kasaita, yana amsawa tamkar sarki a gidan sa. In na gama yakan ce “toh ko kefa”, nakan bishi da “ina mai biyayya Sardauna, ɗan Alkali, ɗan magajin Malam, jikan Malam, Surkin farin Boka ” mostly a wannan gaɓar mukan tuntsure da dariya sai yace to zo nan ya jawoni jikin sa.

Cikin gaisuwan safiya da nake masa wadda mostly in ya dawo daga sallan Asubane, nakan hada da ya Maman ka da Baban ka, yakance min suna lafiya, yanzu na gaishe su wadda yake nufin ya musu addu’a.

Bai taba dawowa gida ban gaishe shi na tambayi wunin hidimar office, wani meeting da na san zasuyi, ko wani challange da nasan suke ciki ba. Wani lokaci in yayi complain din wuya akan wani aiki da sukayi ko challange da yake dashi da wani, nakan ce masa “su bar wahalar min dakai wallah dan kar su tsufar min da kai haka kawai ” ko ince in fa wane bai bar damunka ba zan kai shi ƙara, haka kawai ina dalili da zai na sa maka ɓacin rai ba dalili ”

Nakanyi hakan dan bashi damar samun nitsuwa da nuna damuwata ga al’amuran rayuwar sa.

Hakan da mukeyi yakan qaramana nitsuwa, kusanci, nishaɗi da zaman lafiya a tsakanin mu, kuma yakan tabbatar min da irin tausayi da kulawarsa gareni.

So Personally mu mun dauki gaisuwa wani koface da muke nuna kulawa da ƙauna a tsakanin mu, ba kofar da in daya baiyi ba an rena shi ko ba’a damu dashi ba.

Akwai cigaba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button