Kannywood

Naɗa Abba El-Mustapha, ungulu da kan zabo – cewar sunusi oscar 442

Advertisment

Sunusi Oscer 442 ya zargi shugaban hukumar tace fina finai ta Kano Abba Al-Mustapha da laifin kauda kai alokacin da ake zagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya kira a matsayin uban gidansu.

Oscer 442 wanda shine babban mai bawa gwamnan Kano shawara kan harkokin masana’antar shirya fina finai da wakoki ta Kannywood, babu Wani dalili da shugaban hukumar zaisa ya bari ana yin wakokin cin mutunci ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a jihar Kano ba.

Naɗa Abba El-Mustapha, ungulu da kan zabo - cewar sunusi oscar 442
Naɗa Abba El-Mustapha, ungulu da kan zabo – cewar sunusi oscar 442 Hoto: abba elmustapha/sunusi oscar 442

Har ilayau, ya zargi El-Mustapha da hada kai da yan jam’iyyar adawa tare da jingine yan Kwankwasiyya da suka sha wahalar kafa gwamnati a gefe…

Muna so yadda hukumar tace fina finai ta baya ta ɓata komai muma munyi amfani da ita wajen gyara komai saboda inda aka hau nan ake son sauka amma matsalar da muke da ita shine mun riga minyi kitso da kwarkwata muna kallon wannan jami’i na muna masa kallon ungulu da kan zabo ne domin tun a lokacin da yazo bai tsaya yayi abu na gyara ba.

Ya biyewa masu maganin sabir da shawara  kuma abinda ya dace yayi da yawan ziyarar ce ziyarar ce da dauka hotuna ba kuma wannan abun yasa mu  mawaka suna waka suna zagin sarakunan mu suna zagin Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso da mai girma gwamna kuma ya zuba musu ido , da yake ma tun ranar aka rakashi zaka ga babu niyar gyara a tsarin domin mutanen da suka rakashi wadancan mutane ne da muke gani sunyi ba daidai ba.

Munka gansu suna murna suna dariya a tare tun daga nan nasan cewa akwai matsala fah idan akwai shawara da zai baiwa Gwamna akan kannywood ita ce ta farko da zan fara baiwa gwamna domin mu fara gyara wannan ɓarakar domin basu son yi abu na tufka da warwara.”

Mai tambaya ya tambaye shi baka ganin wannan yayi kira ne na azo a hadu a gyara?

Kai a yanzu Nigeria ka taba ganin an baiwa mutum muƙami wani dan jam’iya ya rakashi kai a ina gani a Nigeria? A yau akwai shugaban moppan na kano state salisu officer ya kirashi yace kana kallon yara suna zagin mai girma gwamna da engr Dr .rabiu musa Kwankwaso ya kamata mu tsaida wannan abun kalma da ta fara fitowa a bakinsa cewa yayi


“Shi bai gani ba, shi bai gani ba shine “

dalilin da yasa na dauki wani clip da aka zagi Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na dora a fegi dina , in bai gani ba za’a gayamasa na saka. sabo ne ankayi bayan an nada tsohon gwamnan kano shugaban jam’iya a jihar kano a zoo road aka ci mutuncin engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso .

Miye amfanin ana zagin iyayen gidan mu a  Kannywood ,miye amfanin mukamin da aka bamu idan munka bari wannan abu yaci gaba wa muke taƙama da shi Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso to an zageshi an zagi gwamnan za’a zagi kowa kuma shine muke gani allon rantsuwar to shine ake masa.

Abinda a nan baima yadda da mu ba domin yanzu bai nemi ba, na dora hotonsa ina taya shi murna bai cemin nagode ba. sai na leƙa yayiwa daso, yayiwa ali nuhu yayiwa mai shadda yayiwa maishinku da duk wani dan APC amma naga nifa dan NNPP ne dan uwanshi dan kwankwasiyya baiyi min ba , nan nago akwai matsala munyi kitso da kwarkwata angulu ne da kan zabuwa.

Zaku iya sauraren hirar kai tsaye a nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button