Ma’aurata : yawan shan maganin karfin maza yana taɓa zuciya – sheikh Adamu Muhammad Dokoro
Ashe Sheikh Muhammad Dokoro yayi kira da nasiha ga ma’aurata musamman idan mutum yayi sabon aure to a gujiya wannnan saboda ba abu ne mai kyau ba.
Mallam ya fara da cewa:
” Wani idan yayi sabon aure yaje ya sayo maganin karfin maza wauta kake yi ai ba da wannan ake dadin jima’i ba kana jahili ba zagi nake ba kayi hakuri dan Allah kanayi abubuwan da baka sani ba har su tabi lafiyar da zuciyarka galibin maganin karfin maza yana taba zuciya kaje ka tambaya likotoci kuma duk wanda zai fiye Shan maganin bature na karfin maza wata rana zuciyarsa na iya bugawa.
Saboda ba’a wannan hanyar ce yakamata kabi ba akwai hanyoyin da ya dace Sa’a nan, shi jima’i shin tuwo ne da kullum sai kaci, ko tuwo an bukaci sai kana jin yunwa sai kaci ba haka kawai ba.
Shin kun san shi azzakarin mutum kamar bororo ne misali idan an yanka kaza a daidai wuyanta akwai inda take tara tsaba to shine bororon kaza, wani cin kazar yake baima san sunanta ba.
Malam ya kara da cewa shi al’aurar namiji idan ya tashi mikewa da idan bai mikeba yake dan kankane amma idan ya miki sai ya zama babba bororon ne yake warware.
Malam yace bari a bar wannan ilimin na musamman ne.”