Ku Biya Haraji Don Ni Bazan Ciwo Bashi Don Yin Aiki Ba-Tinubu Ga Yan Najeriya


Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen dogaro karbo bashi domin gudanar da manyan aiyuka a tsakanin al’umma.
Ya yi magana a ranar Talata a wurin kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji.
Jaridar Dimokuradiyya na ruwaito Kwamitin, wanda aka kafa a ranar 7 ga Yuli, 2023, yana karkashin jagorancin
Taiwo Oyedele, kwararre kan manufofin haraji da kasafin kudi.
Kwamitin wanda ya kunshi kwararru daga bangarori masu zaman kansu da na gwamnati, yana da alhakin sassa daban-daban na sake fasalin dokokin haraji, tsara manufofin kasafin kudi da daidaitawa, daidaita haraji, da sarrafa kudaden shiga.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ya ce kwamitin ya yi daidai da alkawarin da ya dauka na kawar da duk wani shinge da ke kawo cikas ga ci gaban kasuwanci a Najeriya.
Sakamakon gazawar tsarin harajin mu na gaske ne kuma yana da muhimmanci,gazawar gwamnati wajen samar da kudaden shiga yadda ya kamata ya haifar da kai tsaye ga dogaro da rancen kudi don aiki ga al’umma inji Tinubu.
Gwamnatina ba za cigaba da dogaro da Karbi bashi ba domin gudanar da manyan aiyuka domin tattalin arzikin kasar yana tangal tangal
Dalilin haka,bashi ya fara cinye wani kaso mafi girma na kudaden shigar da gwamnati ke samu.
Hakan ya sanya tattalin arzikin kasar cikin wani mummunan yanayi na karbar bashi don biyan bashin da ya gabata kuma ya bar kusan babu wata hanyar ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
A matsayina na shugaban kasa, na kuduri aniyar kawo karshen wannan zagayowar. A ranar da aka rantsar da ni, na yi alkawarin cewa gwamnatina za ta magance dukkan matsalolin da ke kawo cikas ga zuba jari da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya
Wannan alkawari ne ya sa na ga kawo karshen tallafin man fetur. Wannan ne dalilin da ya sa Babban Bankin kasar ya yi kira da a kawo karshen tsarin canjin kudi.
Dalili daya ne muka taru a yau don kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji.”
A nasa bangaren, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, Zacchaeus Adedeji, ya ce kaddamar da kwamitin zai ba shi damar kara tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban-daban domin gano bakin zaren da ke damun manufofin haraji da na kasafin kudi.
Shima da yake jawabi a wajen taron, Oyedele ya ce wadanda suka kaucewa biyan haraji suna cutar kasa kuma ya kara da cewa akwai bukatar a samu sauyi.
Ya ce yan Najeriya a shirye suke su biya haraji idan suka ga abin da ake yi dashi ya amfani kowa.