Hukumar Tace Finafinai Ta Rufe Sutudiyon Mawaki Ɗanzaki
Hukumar ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar tare da yin awon gaba da kayan aikinsa.
Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ita ce ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar nan Idris Ɗanzaki tare da yin awon gaba da kayan aikinsa.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Lawan Sulaiman ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bayan mawaƙin ya yi biris da gayyatar da ta yi mana na bayyana a ofisoshinta.jaridar aminiya na ruwaito.
Ya ce tun ranar Asabar Hukumar ta nemi mawakin ya bayyana a ofisoshinta, amma har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari bai amsa gayyatar ba.
“Kasancewar a yanzu zamani ya sawwa
Sai dai a maimakon ya kawo kansa sai ya turo lauyansa wanda ya zo yake neman bayani shin da gaske ne hukumar tana neman mawaƙin.
“Duk da cewa mun fahimci ya ɗauki lamarin da wasa, amma shugaban hukumar, Abba Almustapha ya nemi a sake gayyatar mawaƙin, amma har zuwa wannan lokaci bai amsa wannan gayyata ba,” in ji jami’in.
Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa Hukumar ta sa aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikinsa.
Sai dai yayin da Aminiya ta tuntubi mawaƙin ya tabbatar mata cewa hukumar ta gayyace shi amma ya tura lauyansa ya wakilce shi.
Bayan sun kira ni a waya sun ce suna gayyata ta, na tura lauyana hukumar don ya wakilce ni.
“Amma me zai faru sai aka kira ni cewa wai hukumar ta rufe sutudiyona haka kuma ta kwashe wasu kayayyakin aikina.”
Mawakin ya yi iƙirarin cewa Hukumar ba ta sanar da shi laifin da take zargin sa da aikatawa ba.
Duk da cewa hukumar ba ta bayyana dalilin gayyatar mawakin ba, amma rahotanni sun nuna cewa ana zargin sa ne da yin munanan kalamai ga jagoran darikar Kwankwasiyya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a cikin wata waka da ya yi a kwanan baya.