Hotuna : Sabon makeken gida da Ɗankareriyar motan Sarkin waka Nazir M Ahmad ya jawo cece kuce
Shahararren mawakin nan Sarkin waka Nazir M Ahmad ya wallafa sabon gidansa da ya gida wanda tabbas wannan makeken gida yaci kudi sosai billiyoyin kudi sosai wanda ba’a magana.
Ga abinda mawakin kuma jarumi ya wallafa akan gidan.
“Sarkin waka mansion Alhamdulillah design by Arch Okosha under supervision of Eng. Nazir and Mustapha T money”
Ga hotunan gida nan.
Mun samu tattara martanin mutane akan wnanan gida da sabuwa motarsa nan.
@auwerlu cewa yake:
Kai har wani alfahari kake d wannan gidan mstwwww gidan bawani gidan bah kazo sae Damien kakuyi d d wani gidan na y kubayi
@muhammad_daha01 cewa yake :@__auwerlu__ talaka uban yan hassada.
@wakili_rgy cewa yake : @__auwerlu__ inba sa a akayi ba duk garin kuma babu irin wannan Gidan kana talaka Amma sai Hassada da kyashi kafita mana kaima kaje kanemi naka.
@ussey_shinkafi cewa yake : Sarkin Waka Namu Maqiyanka fada wanka Ubangiji allah kara daukaka.
@mustapha_s_malik cewa yake : @sarkin_wakar_san_kano Masha Allah Allah yasa alkhairi Amma Dan Allah sarki adauri arinka taimaka alumar annabi s a w bawai Gina manyan gidaje komai kudin mutum idan baitaimaka jama a to akwai matsala.
@king_umar_farouk cewa yake : Allah ya ninka sutura oga Allah ya Kara daukaka da basira daga Umar farouk na naziru sarkin waka.
@deejabeb cewa take : Masha allah sarkin waka Kuma governor waka Baba na shuuuu allah tsaremin kai a duk inda kk @sarkin_wakar_san_kano kana basu ciwo fa a tsaya haka kar Suga ciki su susuce.
@hajaru Muhammad cewa take : Y sunan motar inaso na binciko kudinta a google.