Hassada ce tasa Darakta Sunusi oscar 442 yake kalubalantar Abba Elmustapha – Darakta Sheikh Isah alolo
Guda cikin masu bada umarni a masana’antar shirya fina finai da wakoki ta Kannywood Sheikh Isah Alolo ya ce, kyashi da hassada ne suka sa takwaranshi Sunusi Oscer 442 ya fito yana kalubalantar sabon shuganan hukumar tace fina finai ta jihar Kano Abba Al-Mustapha.
Acewarsa, kamata yayi ya hada kai da sabon shuganan hukumar wajan kawo cigaba, domin kama mutane a daure kamar yadda gwamnatin baya tayi ba shi ne mafita ba.
Alolo, ya bayyana hakan ne a shirin Nishadi@360 na ranar Asabar a Kanawa Radio. yadda hirar darakta Sheikh isah alolo da gida rediyo na kasance.
“Wato maganar Sunusi oscar 442 da kake yi cewa anyi kitso da kwarkwata a wannan kujerar sune kwarkwata din saboda wa kaji ya fito ya soke shi daga yan kwankwasiyya din da wanda ba yan kwankwasiyya ba, babu wanda ya soki abba elmustapha ko wannan kujerar”
Mai Gabatarwa: kasani ko su tsoro suke ji Shiyasa basu fito sunka fada ba.
“Kai kayiwa kanka adalci ace duk yawan yan kannywood shine yafi kowa rashin tsoro, Wannan duk mai hankali yasan idan ya baje a faifai , mutum baiyi kuskure ba ko yaushe ma ya hau kujerar mu dukkanmu nan ba jami’yar mu daya da abba ba, mun masa murna mun masa fatan Alkhairi Sa’a nan muna cigaba da yi masa babu hassada ko kyashi saboda muna masa kyakkyawan fata.
Mai gabatarwa: to shi kyashi yake masa kenan?
“Ai maganganu da yake fada sun nuna hakan saboda idan kana da shawara tunda yace sune yan gaba gaba kamata yayi yaje ya same sa ba magana bace ta kafito midiya kana aibata mutum ba kamar kana so kaci dunduniyarsa ne tun daga lokacin da ya samu muƙamin saboda kwanansa nawa kan kujerar saboda yana yawon kasan miye manufarsa kasan ƙudirinsa sai ka bashi uzuri.”
Ma Gabatarwa : sheikh alolo idan kayi hirar da munkayi zakaji yace har ƙungiyar su ta yan kwankwasiyya amma shi shugaban bai ma basu damar a sauraresu balantana a karbi shawarwarinsu ba.?
“Shi miyasa bai ze ba.”
Mai Gabatarwa: ba’a kira shi ba
“Ai mu ba kiramu yayi ba, duk munje ne ae alaka ake dubawa ta abun farin ciki da ya samu mutum idan kana da shawara ka bayar, ae ba kiranmu yayi ba. Ae a lokacin da yayi fustin a soshiyal midiya yace naya gayyatar duk yan uwa da abokan arziki da duk yan Kannywood da su zo su rakashi ofis dinsa ae harka ta yan Kannywood yanzu ka kira wannan ka kira Wannan ta wuce, amma kana dauka kace duk yan uwa da abokan arziki shikenan ka gayyaci kowa amma tsakaninsa da shi har sai ya kirashi a waya zai je, yanzu duk abinda zakayi bazaka iyawa dan adam ba.”
Darakta Sheikh isah alolo yayi maganganu da dama zaku iya sauraren firar tasu domin wnanan kadan daga ciki ne munka kawo muku ga faifan hirar nan ku saurara.