Bayan Makancewa, Shahararran Dan Wasan Barkwancin Hausa, Karkuzu Na Bodara Ya Tsinci Kan Shi A Mawuyacin Hali
Mallam Karkuzu na Bodara Wanda aka Fi sani da Mallam Shu’aibu Abdullahi Karkuzu yana cikin mawuyacin hali inda yake fama ciwon makanta bayan likitoci sun tabbatar mishi da cewa ya rasa idon shi har abada.
Wani abin tausayi, gidan da Karkuzu yake ciki an saka shi a kasuwa ana so a siyar a kan farashin miliyan 10 kamar yadda mai gidan ya shaida wa wakilan Zinariya. Yanzu ba wannan bane a gaban mu. Abinda muke so shine a fara siyawa Baba Karkuzu abinci domin ya shaida mana cewa akan kwana ba a ci abinci a gidansa ba lura da karfin shi ya kare Kuma makanta Kuma bashi da mataimaki sai Allah.
Da wannan gidauniyar tallafawa ta Zinariya ta ga bukatar neman taimako wajen al’umma domin taimakon Baba Karkuzu.
Zinariya TV sunyi hira da shi akan yadda rayuwa ta sauya masa.
Ga account number nan da lambobin waya ga duk Wanda yake son taimakawa.
Baba Karkuzu yana zama a Jos ne. Duk wanda yake son ganawa shi zamu hada shi da Baba.
Account: 2042684637
Name: Saleh Auwal Ibrahim First Bank
08032911337
08031866089