Babban burina a rayuwa shine na zamo shubabar ƙasa mace ta farko a Nigeria ko gwamna a jihar kano – zainab nasir


Fitacciyar matashiyar ƴar gwagwarmayar nan wacce ta yi suna wajen jawo cece-ku-ce musamman a sabbin kafafen sadarwa na zamani (Social Media), da ƙoƙarin kare haƙƙin al’umma da ayyukan jinƙai, Zainab Nasir Ahmad ta bayyana cewa ba ta da wani buri a rayuwarta da ya wuce ta ga ta Shugabanci Nageriya ko kuma ta zama gwamnan Jihar Kano domin ta shawo kan matsalolin da su ka gagari maza.
Zainab ta bayyana haka a ya yin tattaunawarta da Dokin Ƙarfe TV, inda ta kuma ƙara da cewa ta na da cikakken fata da ƙwarin gwiwar cewa burinta na zama shugabar ƙasa ko gwamnan Jihar Kano zai cika. “Ba na damuwa da maganganun mutane a kaina, domin ina hango nasara, na kuma tabbata zan kai ga cimma burina”. Cewar Zainab Naseer.


“Ina son mulkar Nageriya ko Jihar Kano domin na kawo ƙarshen matsalolin da su ka dame mu kamar matsalar fyaɗe ga yara da mata da matsalar rashawa da cin hanci da kuma matsalar ta’addanci waɗanda maza sun gaza magance su. Ina da burin ganin na bunƙasa tattalin arziƙi tayadda matasa za su samu ayyukan yi na kawar da talauci a Nageriya ko Jihar Kano jama’a su rayu cikin walwala da cigaban rayuwa ta kowane fanni”. Cewar Zainab Naseer.
Dangane da gurguwar fahimtar da wasu Al’umma su ke da ita kan shugabancin mata kuwa, Zainab ta bayyana cewa “ko a tarihin Musulunci na can asali mata ba ƙashin yasarwa ba ne a fannin ba da gudunmawa ga cigaban al’umma. Misali:
Manzon Allah (S.A.W) ya samu nasarar yaɗa addinin musulunci da gudunmawar mata iyalinsa. Matarsa Nana Khadija gawurtacciyar ƴar kasuwa ce wacce Allah Ya azurta da tarin dukiya. Nana Khadija ta taimakawa manzon Allah (S.A.W) da gudunmawar kuɗin gudanar da da’awa da gudunmawar shawarwari da gudunmawar kykkyawar ɗabi’a tare da ƙarfafa masa gwiwa kan aikinsa na isar da saƙon Allah (Manzanci), wannan wani misali ne da ke nuna jarumta da sadaukarwar mata kan al’umma”. Cewar Zainab.
Zainab ta kuma ƙara da cewa: “Ko da a fannin ilimi da karantarwa ba a bar mata a baya ba domin kuwa mafi yawan shahararrun malaman da su ka tattara hadisan manzon Allah (S.A.W) a farko-farko mata ne su ka karantar da su. Misali: Ibn Hajar ya ɗauki darasi a wurin mata kimanin 53. Shi ma As-Sakhawi ya yi karatu a wurin mata kimanin 68. Imam Suyuti shi ma ya yi karatu a wurin mata kimanin 33”. Inji ta.
Daɗi da ƙari Zainab ta kuma ƙara da cewa: “Manzon Allah (S.A.W) ya karantar cewa kamar yadda ƴaƴa maza su ke da ƴancin rayuwa da samun ilimi da sauran haƙƙoƙi, haka su ma ƴaƴa mata su ke da wannan ƴanci. Babu wani wanda ya fi wani a wurin Allah sai wanda ya fi wani taƙawa da tsoron Allah. Da’awar manzon Allah (S.A.W) ita ce ta samarwa ƴaƴa mata ƴanci ta wayar da kan larabawan zamanin jahiliyya su ka dena binne su, saboda haka wannan ya isa misalin da al’umma za su fahimci cewa maza da mata kowa ya na da dama da ƴancin neman shugabanci”. Inji ta.
A dangane da cancanta da kuma kwalitin shugabanci kuwa, Zainab ta bayyana cewa “mata sun cancanta a ba su kowacce irin dama ta shugabancin al’umma domin kuwa a wani rahoton bincike da aka fitar, tsakanin Maza da Mata su waye su ka fi cancanta su shugabanci Al’umma a tsarin shugabancin Siyasa ?
Sakamakon ya nuna cewar kashi shida (6%) na mutane (2,250) da aka ji ra’ayinsu sun bayyana cewa mata sun fi cancantar su zama shugabannin siyasa fiye da maza. Sannan mutum ɗaya cikin mutane biyar, kashi (21%) sun bayyana cewa maza sun fi mata cancantar zama shugabannin siyasa. A ra’ayi na bai ɗaya kuma, kaso sittin da tara (69%) sun bayyana cewa babu bambancin kwaliti ta fuskar cancantar shugabancin siyasa a tsakanin maza da mata, gaba ɗaya ƙwalatinsu ɗaya ne maza ba su fi mata ba, mata ma ba su fi maza ba, kenan za mu iya har ma mu fi mazan yin abin azo a gani”. Cewar Zainab Naseer.
Daga ƙarshe Zainab ta buƙaci al’umma da su cigaba da yi mata addu’a su kuma ba ta haɗin kai da goyon baya domin ganin burinta ya cika ta samu nasarar magance matsalolin da maza su ka gaza magance su a wannan ƙasa.