Amarya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Har Lahira Ana Tsaka Da Shagalin Bikinta
Wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun ta mutu a ranar daurin aurenta a garin Ogbomoso na jihar Oyo.
Mummunan lamari ya faru ne a jajibirin daurin auren marigayiyar a lokacin da ake shagali da bireɗan biki tare da kawayenta.jaridar dimokuraɗiyya ya ruwaito.
A cewar mahaifin marigayiyar, Evangelist Oyedotun na cocin C&S Reformed, da ke Isale-High School, Amaryar kwata kwata ba ta nuna wani alamun rashin lafiya a baya ba har sai da ta faɗi da misalin karfe 10:30 na safe kafin ta rasu, sai daga baya kuma amaryar ta rasu
Ɗaurin auren Abiodun Oluwadamilare a ranar Asabar, 19 ga Agusta, 2023.
Iyayen angon sun yi wa saniya yankan rago a Ogbomoso, kuma kasancewar ango daya tilo, Abiodun, angon ya yi farin ciki, bai san cewa ajalin amaryar ya ɓuya a bayan ƙofa ba.
Duk da cewa mahaifiyar marigayiyar, Misis Ruth Oyedotun, ta kasa magana saboda bakin ciki, mahaifin, Evangelist Oyedotun ya bayyana cewa sun dauki amaryar nan take bayan ta faɗi zuwa asibitin koyarwa na LAUTECH domin ceto rayuwarta har a kammala bukukuwan aure.
“Mun kai ta asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomoso. Bayan wani lokaci, ta farfado, har zuwa wayewar garin Asabar, yanayinta ya tsananta don haka ta kebe kan gado.
“An ma bukaci mu kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bowen don yin wasu gwaje-gwaje, wanda muka yi ba tare da bata lokaci ba.
“Angon ya suma, yana kuka, ya ce, ‘Bari in tafi da ita.’
“Muna kwance a asibiti a tsawon wannan Asabar.
Rashin lafiyarta ta kara tsananta har sai da ta riga mu gidan gaskiya, a cewar Tori News.
A cewar ‘yar uwar angon, shirye-shirye sun yi nisa kafin faruwar lamarin.