Farashin kwandon Tumatir ya kai N100,000 a Legas
A Nijeriya farashin Tumatir da barkono da sauran kayan miya sun yi tashin gwauron zabo a wasu manyan kasuwannin jihar Legas.
Yayin da ake sayar Kwandon tumatir tsakanin N90,000 zuwa N100,000, sabanin yadda ake sayar da shi a da kan N20,000 a baya.
Haka nan kuma kwandon tattasai da aka fi sani da “Rodo” wanda a da ana sayar da shi tsakanin Naira 12,000 zuwa Naira 15,000, yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 40,000 zuwa Naira 45,000, gwargwadon irin kyaun sa.
Wasu mata yan kasuwa a unguwar Egbeda da ke Alimosho suka tabbatar da tashin farashin ga majiyar DCLHausa ta jaridar Tribune.
Haka kuma ‘yar kasuwa Ronke Saliu, wacce ke sayar da wadannan kayayyaki a tashar mota ta Bammeke da ke unguwar Shasha, ta bayyana cewa karin farashin ya kuma shafi launin barkonon nan da ake kira “Bawa,” wanda kudinsa ya haura zuwa N55,000 daga farashin baya na N15,000 zuwa N20,000 da ake sayarwa.