Bidiyon Uba yana tika rawa da yarsa wajen auren ta ya jawo cece kuce ga Al’umma
A wani bidiyo da shafin arewa fashion style sunka wallafa uba da yarsa amarya suna ta tika rawa abun ya baiwa mutane matukar mamaki.
Irin yadda mahaifin yarinyar ya shigo da ita a dandalin bikin yarsa yana da kwasa rawa ana musu hadari na nairori shine ya sanya mutane to albarkacin bakisu.
Hausaloaded ta tattaro muku kadan daga cikin martanin mutane akan wannan bidiyo.
@Muhammad shamsuddeen Gumau cewa yake : Fulawar juji, Allah kar kasa mu auro a irin wannan gidan!
@ khalifa bashir Ginin gold cewa yake : Ya Allah
Kar Ka Kama Mu Da Laifin Da wawayen Cikin Mu Ke Aikatawa
@sadiya adam sulaiman cewa take : Sai kayi mgn ace bakin ciki gareka da kuma talauci amma dai anji kunya kuma wannan abin kuka ne
@Isah Ibrahim yana cewa : Allah ya tsinewa wannan wayewar, shi kuma mahaifin nata Allah ya shirye shi ya ganar dashi.
@mukhtar s yahuza cewa yake: Duk wata wayewa wacce ba daga koyarwar manzon Allah da sahabbai tasamo asali ba Allah ubangiji yayi mana tsari tareda gina katangar karfe tsakaninmu da ita.
@zakariyya abbati rafin dadi yana mai cewa : Alhamdulillahi Allah mungode maka da kasa dattawa ne suka haife mu .
@abdulmutallib hamza kibiya yana cewa : Idan ace muku Kuji tsoron Allah ku ƙulla Aure yadda addinin musulunchi ya umarce ku, Sannan ku guji idanu Da bakin Miyagun Mutane baza Ku yarda ba. Sai a jera Sati guda Ko fiye Da haka ana ta faman events Kala Kala ana sabawa Allah ta’ala Wai Duk a Cikin hidimar Aure.
Wai shin waye Kuka ga ya wofantar Da Faɗin Allah da Manzonsa kuma haƙarsa ta cimma ruwa?
To Gani ga wane……