Ali Nuhu ga Davido: Ka goge wakar nan ka kuma nemi afuwar Musulmai
Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood da na Nollywood, Ali Nuhu ya shawarci mawakin nan Davido da ya cire wani faifan wakar da ya janyo cece-kuce tare da neman gafarar musulmi.
Mawakin na fuskantar suka daga Musulmai bayan ya wallafa tsakuren wakar da ya yi shi da sabon yaronsa mai suna Logo Olori, a waka mai taken ‘Jaye Lo.
Musulmai a fadin Nijeriya sun zargi mawakan da rashin mutunta addinin musulunci a cikin wakar.
Faifan bidiyon mai tsawon dakika 45 ya nuna wasu maza sanye da fararen jallabiya da hula suna rawa a gaban masallaci, maimakon yin sallah.
Da ya ke magana a kan lamarin, Ali Nuhu, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi kakkausar suka ga Davido, inda ya nuna allawadai da wakar.
Ya ce dole ne masu nishadantar da al’umma su koyi mutunta addini, al’adu, da al’adun sauran mutane.
“Na ci karo da faifan bidiyo mai cike da cece-kuce da @davido ya yi, kamar yadda muke so, mu rika nuna fasahar mu a fannoni daban-daban, ya kamata mu koyi mutunta addini, al’ada, da al’adar wasu. Wannan ba abin yarda ba ne kwata-kwata a Musulunci. Ya kamata ku cire wannan bidiyon ku ba da hakuri kan cutar da al’ummar musulmi baki daya,” ya rubuta.