Kannywood

Abba Kabir Yusuf Ya nada Abba Elmustapha a matsayin Shugaban tace fina finai

A yau din nan ne majiyarmu ta hausalaoaded ta samu labarin daga Premier Radio kano labrin cewa Abba Elmustapha ne ya samu zama shugaban tace fina finai a jihar kano (chairman censorship board)

Abba El-Mustapha1 dai guda ne daga cikin jaruman fina-finan Hausa na Kannywood wanda ya jima a tsarin siyasar Kwankwasiyya.Abba Kabir Yusuf Ya nada Abba Elmustapha a matsayin Shugaban tace fina finai

Daman dai tuni hankula suka karkata kan wanda za’a bawa hukumar, yayin da wasu ke tunanin za’a bawa Sunusi Oscar 442, kasancewar yana cikin na gaba-gaba a sha’anin siyasar ta Kwankwasiyya a Kannywood.

Wasu daga cikin jaruman Kannywood dai sun sha fuskantar dauri a gwamnatin baya, abinda aka alakanta da yadda ake zarginsu da nuna zazzafar adawar siyasa ga tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC a wancan lokaci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button