Wata matashiyar budurwa tace Baza Su Dena Yin Ciko ba martani zuwa ga Aisha Humaira
Wata fardediyar budurwa mai suna Halima Shehu tace baza su dena yin ciko da kayayyakin da zasu dunga sauya musu jiki ba.
Hakan ya biyo bayan wata shawara mai kama da kashedi da wata jarumar Kannywood, Aisha Humaira ta baiwa Yan mata musamman matan Kannywood dake yin ciko.
Jarumar ta nuna damuwa sosai a wani faifayin Bidiyon daya karade kafafen sadarwa, inda take baiwa matan shawara da cewar su dunga fitowa yadda Allah ya halicce su ba tare da sun sanya ciko a duwawu ko wani sassa na jikin su da zai daga darajar jikin su ba. Jaridar dimokuraɗiya na ruwaito a shafinta na facebook.
Tace hakan na jawo rikita rikita bayan Aure idan maza sun fahimci cewar ba abun da suka aura suka gani ba, ganin cewar wasu mazan suna la’akari da diri wajen Auren mace.
Duk dadai a yayin shawarar tata ta baiwa Mata hakuri, to amma matashiyar mai suna Halima Shehu, tace baza su dena yin ciko ba.
Rahotanni sun bayyana cewar kashi mai tsoka na Mata da Yan mata suna amfani da kayayakin dake daga darajar jikin su misali kamar Mama (Nono) da Mazaunai da abun matse ciki wanda ake siyarwa a shaguna.