Addini

Malamina Yana Sauke Alƙur’ani A Ƙasa Da Rabin Awa (30minutes)– Sheikh Prof Maƙari

Mataimakin babban limamin Babban Masallacin Abuja, Sheikh, Farfesa Ibrahim Maƙari ya bayyana cewa Malaminsa yana sauke Alƙur’ani mai cikin ƙasa da rabin awa.

Fitaccen malamin ya faɗi haka ne a cikin wani faifan bidiyo, inda yake magana kan irin baiwa da karamar da Allah Ya ba Malaminsa. Duk da cewa bai ambata sunan malamin nasa ba, amma ya ce yana ɗaya daga cikin mafi kusa da shi.

 

Malamin ya nuna cewa wasu za su yi mamaki a ce wani ya sauke Alƙur’ani a ƙasa da minti 30, to amma a cewarsa, wannan ba abin mamaki ba ne ga wanda Allah Ya hore ma wa.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button